Ya gudu ya bar matarsa don ta haifa masa ’ya babu hannaye
Wani mutun mai suna Mudashir Sheriffdeen mutumin jahar Ogun ya arce a locakin da ya tabbatar da cewa matarsa ta haifi yarinya da kafada kawai ba hannu guda biyu. Sheriffdeen wanda ya ke zaune a inda ake kira Bosun Street, a karamar hukumar Ife a jihar Ogun an ce ba a ganshi ba tun ranar […]
Wani mutun mai suna Mudashir Sheriffdeen mutumin jahar Ogun ya arce a locakin da ya tabbatar da cewa matarsa ta haifi yarinya da kafada kawai ba hannu guda biyu.
Sheriffdeen wanda ya ke zaune a inda ake kira Bosun Street, a karamar hukumar Ife a jihar Ogun an ce ba a ganshi ba tun ranar talatar da aka bashi labarin haihuwar.
Matar Sheriffdeen ta ce minin nata ya arce ne lokacin da ya ji ta haifi da ba hannaye sai kafada. “wannan shi ne da na na farko, bansan dalilin da ya sa na haifishi ba hannaye ba. Tun lokacin da mijina ya sami labarin abin da na haifa bai kara zuwa ya ziyarce ni ba”.
“Mijina yana sana’ar tukin motane kuma mun yi aure tsahon shekaru biyu kenan ubangiji da ya tashi amsa addu’ar mu ga abin da ya bamu.
Matar wadda ba’a fadi sunanta ba ta ce duk wata shawara da likitoci suka bata lokacin da take da ciki ta yi amfani dasu.
Ta ce a halin yanzu asibitin da take sun sallameta kuma gidan da suke haya masu gidan sun aikomata cewa kada ta kuskura ta koma gidan su bayan ta fito da ga asibiti.
Wasu daga cikin makusanta mijin an ji suna cewa yana ikirarin cewa wannan ba danshi ba ne.