Ya guje wa matarsa don kada kukan jaririya ya dame shi
Wata gyatuma mai shekara 60 a qasar Serbia ta haihu bayan shekara 20 tana ta hanqoro, amma mijinta ya yi watsi da ita don gudun kada kukan jariri ya qara tsananta cutattukan da yake fama da su, a cewarsa. Atifa Ljajic har ta fitar da qaunar samun haihuwa sai likitoci suka sanar da ita cewa […]
Wata gyatuma mai shekara 60 a qasar Serbia ta haihu bayan shekara 20 tana ta hanqoro, amma mijinta ya yi watsi da ita don gudun kada kukan jariri ya qara tsananta cutattukan da yake fama da su, a cewarsa.
Atifa Ljajic har ta fitar da qaunar samun haihuwa sai likitoci suka sanar da ita cewa tana da juna biyu, sanadiyyar dashen qwayayen haihuwa da aka yi mata. Kuma ma’auratan sun samu gudunmuwar maniyi. Don haka take cike da farin cikin samun ’ya da ta sanya wa suna Alina, amma hankalinta ya dugunzuma ya tashi saboda mijinta Serif Nokic mai shekara 68 ba zai iya jure kukan jariri ba, kamar yadda ya faxa mata.
A hirar da aka yi da shi, Serif ya ce: “Ta samu abin da take so, yanzu tana cikin farin ciki.
Ya ce yana fama da larurar rashin lafiya, wadda ta haxa da ciwon suga da ciwon zuciya. Don haka yake ganin zai samu matsalar yin barci da daddare idan jariri na kuka.