Ya gurfana a kotu bisa zargin cinna wuta a dakin da mutum 3 ke barci a ciki
Wani matashi mai shekara 30 da ke zaune a garin Gwagwa a Abuja, ya gurfana a gaban Kotun Lardi ta Gwagwa bisa zarginsa da cinna wa wani daki wuta a yayin da wasu mutum 3 ke barci a ciki da tsakar dare. dan sanda mai gabatar da kara, Saje Noah Moses na babban ofishin ’yan […]

Wani matashi mai shekara 30 da ke zaune a garin Gwagwa a Abuja, ya gurfana a gaban Kotun Lardi ta Gwagwa bisa zarginsa da cinna wa wani daki wuta a yayin da wasu mutum 3 ke barci a ciki da tsakar dare.
dan sanda mai gabatar da kara, Saje Noah Moses na babban ofishin ’yan sanda na Gwagwa ya shaida wa kotun a shekaranjiya Laraba cewa, wata mai suna A’isha Abdullahi da ke zaune a gida daya da mutumin, ta shigar da kara a ofishinsu a ranar 6 ga Nuwamba inda ta ce “Kai Kazeem Kareem ka cinna wa dakinta wuta a ranar kuma a sakamakon haka, mutum 3 da ke barci a ciki da suka hada da ’yarta mai shekara 3 mai suna Blessing Dele da ’yar uwarta mai shekara 16 mai suna Aino Ojo da kuma kawarta Bosse jimoh, sun samu konewa mai tsanani, haka daukacin kayanta da ke cikin dakin sun kone sakamakon wutar.
Da alkalin kotun Mai shari’a Muhammad Adamu Wakili ya waiwayi Kazeem ya musanta zargin da a ke yi masa. Daga nan dan sanda mai shigar da kara ya bukaci da a dage shari’an zuwa gaba, inda bangarori biyu za su gabatar da shaidunsu. Sai dai lauyan wanda ake zargi ya bukaci a ba da belinsa a yayin da mai shigar da kara a bukaci da a ci gaba da tsare shi. Ya bayyana wa kotun cewa kasancewar kotun za ta so ta ji daga bakin mutum ukun da a halin yanzu ba sa kusa, akwai bukatar a ci gaba da tsare wanda ake zargi har zuwa gaba don ba su damar bayyana a kotun.
Ya ce mutum ukun da suka kone wadanda da farko aka kai su Babban Asibitin Gwarinpa bayan kai su wani asibiti da ke Gwagwa, an tura su zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abuja da ke Gwagwalada, amma a can ma sai a ka bukaci a kai su Asibitin kashi da ke Enugu sakamakon munin kunar da suka yi. Ya ce wanda ake zargin idan aka ba da belinsa, zai iya shisshigi ga binciken da ake yi ko ya sulale saboda munin abin da ake zarginsa da aikatawa.
Mai shari’a Wakili ya yi watsi da bukatar belin, inda ya umarci da a ci gaba da tsare shi har zuwa ranar 20 ga Nuwamba inda za a ci gaba da sauraren shari’ar.