Ya gurfana a kotu bisa zargin karya hannuwan jariri
Wani mutum mai suna Francis Audu mai shekara 30 da ke zaune a yankin Double Pool a garin New Nyanya da ke Jihar Nassarawa, ya gurfana a gaban Babban Kotun Jihar da ke garin Mararraba, inda ake tuhumarsa da karya hannuwa biyu na wani jariri mai wata hudu da haihuwa. dan sanda mai gabatar da […]
Wani mutum mai suna Francis Audu mai shekara 30 da ke zaune a yankin Double Pool a garin New Nyanya da ke Jihar Nassarawa, ya gurfana a gaban Babban Kotun Jihar da ke garin Mararraba, inda ake tuhumarsa da karya hannuwa biyu na wani jariri mai wata hudu da haihuwa. dan sanda mai gabatar da kara Saje Joseph Ahu’a na babban ofishin ’yan sanda da ke garin Mararraba ya shaida wa kotun a shekaranjiya Laraba cewa mahaifiyar jaririn mai suna Francisca Oboy ta kai kara ofishinsu inda ta ce a ranar 6 ga Oktoba ta danka jaririn a hannun Francis a lokacin da take yunkurin ceto wata ’yarta da wata yarinya mai suna Blessing ke duka, amma kafin dawowarta sai ya karya hannuwan jaririn guda biyu. Hakan ya saba wa sassa na 97 da 246 da 95, da kuma 238 na dokokin Penal Code.
Da Alkalin kotun Mai shari’a bincent W. Gwahemba ya waiwaye wanda ake tuhumar ya musanta zargin, daga nan ne alkalin ya ba da umurnin a wuce da shi zuwa kurkuku, har zuwa ranar 30 ga wannan wata don ci gaba da sauraron karar.