Ya gurfana gaban kotu saboda neman matar aure
A ranar Juma’ar da ta gabata ne Kotun Shari’ar Musulunci da ke Sabon Gari ta fara sauraron tuhumar da ake yi wa wani mutum mai suna Sani Lawan mazaunin Unguwar Birged da ke Kano bisa zarginsa da laifiin neman matar aure. Mai gabatar da kara Shehu Adamu ya bayyana wa kotu cewa a ranar 13 […]
A ranar Juma’ar da ta gabata ne Kotun Shari’ar Musulunci da ke Sabon Gari ta fara sauraron tuhumar da ake yi wa wani mutum mai suna Sani Lawan mazaunin Unguwar Birged da ke Kano bisa zarginsa da laifiin neman matar aure. Mai gabatar da kara Shehu Adamu ya bayyana wa kotu cewa a ranar 13 ga Yunin bana ne iyayen matar da suka hada da Sabo Ya’u da Alhaji Alhassan da Sa’adatu Alhassan suka kai wa ’yan sanda kara cewa suna zargin Sani Lawan da boye musu ’ya, wacce kuma matar aure ce ga Malam Umar. Ya ce iyayen matar sun ce sun samu labarin ne ta hanyar wadansu mutane da suka kira su a waya suka kuma sanar da su cewa sun ga ‘yarsu wacce ta bace tare da wanda ake zargi a wani dakin hotel da ke Unguwar Birged.
Mai gabatar da karar ya ce aikata hakan laifi ne da ya saba wa sashi na 173 na Kundin Shari’a na Jihar Kano. Da kotun ta waiwayi Sani Lawan ya yarda da duk abin da aka fadi a cikin takardar karar. Ita ma a nata bangaren matar (wacce aka boye sunanta) ta bayyana wa kotu cewa ita ce ta kai kanta wajen wanda ake zargin bayan maigidanta ya sake ta. Mai shari’a Abdu Abdullahi Waiya ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake zargin a gidan maza, sannan ya dage sauraren shari’ar zuwa 22 ga watan Yuli.