Ya gutsure hannunsa saboda zafin ciwo

Wani mutumin Ingila mai suna Mark Goddard ya kirkiro da wata na’urar da ya yi amfani da ita wajen gutsure hannunsa na hagu saboda raunin da ya samu a wani hadari da ya rutsa da shi kimanin shekara 16 da suka gabata. Goddard, mai kimanin shekara 44 ya kirkiro da na’urar ce da ke dauke da […]

Ya gutsure hannunsa saboda zafin ciwo

Mark Goddard from Devon who chopped his own hand off with a home made guillotine to try to end years of pain from a motorbike accident. See SWNS story SWHAND: A road accident victim plagued by nerve pain has horrifically chopped off his own hand – using a homemade GUILLOTINE. Desperate Mark Goddard, 44, says […]

Wani mutumin Ingila mai suna Mark Goddard ya kirkiro da wata na’urar da ya yi amfani da ita wajen gutsure hannunsa na hagu saboda raunin da ya samu a wani hadari da ya rutsa da shi kimanin shekara 16 da suka gabata.
 Goddard, mai kimanin shekara 44 ya kirkiro da na’urar ce da ke dauke da adda da zaren lilo da kuma wasu kusoshi wajen amfani da ita don gutsure wuyan hannunsa na hagu don ya huta da radadin da ya dade yana yi masa saboda raunin da ya samu a wani hadarin mota da ya rutsa da shi.
Sai dai abin mamaki shi ne yadda mutumin ya ki yarda ya ziyarci asibiti don likitoci su duba shi ta hanyar yi masa maganin da zai iya warkewa a duk tsawon shekarun da ya kwashe tare da raunin.  A ganinsa da ya je asibiti likitoci su kara jagwalgwala masa hannun, ya gwammace ya bi hanya mafi sauki ta datse hannun don ya huta da radadin.  Hakan ta sa ya kwashe lokaci mai tsawo yana tunanin hanyar da zai bi don ya samu biyan bukata, inda daga karshe ya yanke shawarar kirkiro da na’urar da ya yi amfani da ita a harabar gidansa.
Sai dai Mark ya samu tangarda a lokacin da na’urar  ta kasa gutsure hannun gaba daya don ta kasa tsinke jijiyoyin da ke hannun al’amarin da ya sa hannun ya rika reto sai da ya yi amfani da sharbebiyar wuka wajen yanke jijiyoyin kafin gundulmin ya fadi kasa.
Rahoton ya ce jim kadan bayan ya gutsure hannun ne sai ya yi amfani da ashana wajen kone dungulmin da ya yanke don kada nan gaba a yi yunkurin sake dasa masa.
Jim kadan da aikata hakan ne sai ya fadi kasa sumamme kuma ihun da ya rika yi kafin ya suma ne ya janyo hankalin makwabta inda suka garzaya da shi asibiti.  Likitoci sun tabbatar ya yi asarar jini mai yawa bayan sun yi nasarar ceto ransa. Likitocin sun bayyana cewa babu yadda za a yi masa dashe a wurin  tun da ya riga ya kona gutsuren hannun, don haka an dinke dungulmin hannun nasa ne kawai sannan aka sallame shi daga asibiti bayan ya samu sauki.
Tuni Mista Mark ya cigaba da rayuwa a matsayin mai gutsurarren hannu kuma ya ce bai yi nadamar abin da ya aikata ba.  Ya ce gwamma ya cigaba da rayuwa a matsayinsa na mai gutsurarren hannu, maimakon rayuwa da hannun da zai hana shi sukuni saboda radadin ciwo.
An ruwaito Mista Mark ba shi da mata balle ’ya’ya, al’amarin da ya sa shi kadai yake zaune a gidansa.