Ya halaka makwabcinsa a kan kudin lantarki

Wani mutum mai suna Felid Omokhoa, dan shekara 36 a duniya yana fuskantar hukunci a kotun majastari da ke Ekpoma, kan zarginsa da kashe makwabcinsa mai suna Richard Ikekhua, a sanadiyyar doka masa bulo a kai.Kamar yadda bincike ya nuna, wannan lamarin ya faru ne a watan Janairun bana, a kauyen Ukpoke Heile da ke […]

Ya halaka makwabcinsa a kan kudin lantarki
Ya halaka makwabcinsa a kan kudin lantarki

Wani mutum mai suna Felid Omokhoa, dan shekara 36 a duniya yana fuskantar hukunci a kotun majastari da ke Ekpoma, kan zarginsa da kashe makwabcinsa mai suna Richard Ikekhua, a sanadiyyar doka masa bulo a kai.
Kamar yadda bincike ya nuna, wannan lamarin ya faru ne a watan Janairun bana, a kauyen Ukpoke Heile da ke karamar Hukumar Ekpoma Esan ta yamma. Wata takaddama ce ta shiga tsakanin magidantan biyu, inda wanda ake zargin ya kashe shi a kan batun rashin biyan kudin wutar lantarki na gidan da suke zaune a ciki; inda ya yi amfani da bulo ya kwabda wa makwabcin nasa a kai yayin da suke cikin fada. A take dai magidancin ya bakunci lahira.
’Yan uwan marigayin ne da wasu na kusa da shi suka shigar da kara gaban kotu. A ta bakin hukumar ’yan sanda  kan binciken da suka gudanar kuma suka mika wa kotu, sun bayyana cewa tun kafin wannan rana da suka yi fada, dama can wanda ake zargi da kisan kan yana da sabani da mamacin. Daga bisani ne takaddamar biyan kudin lantarki ta shiga tsakaninsu, har al’amarin ya kai ga kisan kai.
Tun farko dai an ce, wanda ake tuhumar ne ya hada kai da sauran makwabta, suka yanke wayar wuta mai kai hasken lantarkin zuwa dakin mamacin. Inda shi kuma sai bai hakura ba, ya hau dokin zuciya ya tafi ya kai kara a ofishin hukumar wutar lantarki na yankin da yin bayanin cewa suna anfani da wutar ba bisa ka’ida ba. A take hukumar ta tura aka yanke wutar baki daya daga gidan da suke zaune a ciki, aka bar su cikin duhu.
Wannan mataki da mamacin ya ya dauka, bai isa ba, inji rahoton; sai ya wuce ya kai kara ga ’yan sanda na shiyyar kuma sai aka sa aka kama shi. Daga bisani an yi masu tsakani da sasanci, aka gargadi wanda ake zargi da cewa kar a ji ya sake shiga harkar mamacin.
Bayan da suka koma gida sai suka sake samun sabani tsakaninsu, suka kaure da fadan da ya haddasa mutuwar mamacin.