… Ya hana bai wa sarakuna da ’yan siyasa takin zamani

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i ya ba da umarnin a daina bai wa sarakuna da ’yan siyasa takin zamani a jihar, inda ya ce duk wanda yake son takin a cikinsu ya tafi kasuwa kamar kowane manomi ya saya. Wannan umarni na dauke ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Mai […]

… Ya hana bai wa sarakuna da ’yan siyasa takin zamani
… Ya hana bai wa sarakuna da ’yan siyasa takin zamani

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i ya ba da umarnin a daina bai wa sarakuna da ’yan siyasa takin zamani a jihar, inda ya ce duk wanda yake son takin a cikinsu ya tafi kasuwa kamar kowane manomi ya saya.

Wannan umarni na dauke ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Mai Gwamnan Shawara a Harkar Watsa Labarai, Samuel Aruwan.
Gwamna El-Rufa’i ya kuma ba da umarnin a rika sayar da takin zamanin kai-tsaye ga manoman jihar, ya fadi haka ne a lokacin da ya kai ziyarar ba-zata wajen ajiyan taki na Hukumar Noma ta Jihar da ke a kauyen dankande a titin Kaduna zuwa Zariya.
“Gwamnan ya ba da umarnin cewa duk takin zamani da ake raba wa sarakuna da ’yan siyasa a daina ba tare da bata lokaci ba. A rika sayar da takin zamanin kai-tsaye ga talakawa manoma a wurin da aka ware domin sayar da taki a jihar. Gwamnan ya kuma ba da tabbataccin cewa ba zai amince da rashin gaskiya da cin amanar talakawa ba,” inji sanarwar.
Ta kara da cewa “Gwamnan ya kuma umarci Ma’aikatar Noma ta Jihar ta samar da takin zamanin ga kasuwa domin a kauce wa karancinsa wanda hakan ka iya janyo cin hanci da rashawa wajen sayar da takin,” inji shi.
El-Rufa’i ya kara da cewa bai dace samar da taki ga manoma ya zama wahala ba.