Ya harbi kansa da bindiga don jin yadda ake ji
A karshen makon jiya ne wasu ’yan sanda a birnin Elda na kasar Spain suka garzaya da wani mutum asibiti, bayan ya harbi kansa da bindiga a kafa da gangan, kamar yadda kafar yada labarai ta Odd News Blog ta bayyana. Kodayake, rundunar ’yan sandan kasar ba ta kai ga bayyana sunansa ba tukuna. Kuma […]
A karshen makon jiya ne wasu ’yan sanda a birnin Elda na kasar Spain suka garzaya da wani mutum asibiti, bayan ya harbi kansa da bindiga a kafa da gangan, kamar yadda kafar yada labarai ta Odd News Blog ta bayyana.
Kodayake, rundunar ’yan sandan kasar ba ta kai ga bayyana sunansa ba tukuna. Kuma ta ce tana ci gaba don neman bindigar da ya yi danyen aikin da ita, kodayake suna zargin cewa ya yi jifa da ita ta tagar motar da aka garzaya da shi asibitin.
Dokar kasar ta za ta bukaci a fara binciken hankalinsa kafin a tuhume shi da laifin amfani da makami. Kodayake, lokacin da ’yan sanda suke masa tambayoyi, mutumin mai kimanin shekara 35, ya ce ya yi hakan ne domin ya ji yadda ake ji idan aka harbi mutum. Amma da farko musanta hakan ya yi, inda ya ce ya yi hakan ne bisa “kuskure.”