Ya ja hankalin ’yan Arewa kan take-taken Obasanjo
Wani na hannun damar Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, Alhaji Abdullahi Sugar ya yi kashedi ga ’yan Arewa da su yi hankali da zargin take-taken Tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo na tilasta wa Arewa zaben yaronsa a zaben shugaban kasa na shekarar 2019. Sugar a wata tattaunawa da ya yi da Aminiya ta wayar […]
Wani na hannun damar Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, Alhaji Abdullahi Sugar ya yi kashedi ga ’yan Arewa da su yi hankali da zargin take-taken Tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo na tilasta wa Arewa zaben yaronsa a zaben shugaban kasa na shekarar 2019.
Sugar a wata tattaunawa da ya yi da Aminiya ta wayar salula ya yi ikirarin cewa tsohon shugaban kasar ya kokarin ko dai ya tsayar da Gwamna Nasir-el-Rufa’i ko kuma Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso daga yankin.
“Mu ’yan Arewa dole mu yi taka-tsantsan ga wannan dabara. Ya faru a baya kuma ba za mu kyale hakan ta sake faruwa ba. Ya zama wajibi shi Obasanjo ya bar mutane su zabi wanda suke so. Me ya sa yake son tsayar da Kwankwaso ko El-Rufai’i bayan akwai ’yan siyasar da suka fi su?.Ya zama dole ya bar mutane su zabi wanda suke so. Ka gaya masa ’yan Najeriya yanzu sun waye a siyasa fiye da shekarar 2017”. Inji shi