Ya je cire kudi a banki na’urar ATM ta nuna ya mutu
Wani dan kasar katar ya gano cewa hukumomin kasar sun fitar da takardar shaidar mutuwarsa, don haka aka rufe asusun ajiyarsa na banki, lamarin da ya sa na’urar ATM ta nuna ya mutu lokacin da ya je cire kudi a banki. Duk da cewa mutumin yana a raye cikin koshin lafiya, bankin da yake ajiyar […]
Wani dan kasar katar ya gano cewa hukumomin kasar sun fitar da takardar shaidar mutuwarsa, don haka aka rufe asusun ajiyarsa na banki, lamarin da ya sa na’urar ATM ta nuna ya mutu lokacin da ya je cire kudi a banki.
Duk da cewa mutumin yana a raye cikin koshin lafiya, bankin da yake ajiyar kudi sun ce “hukuma ta tabbatar da mutuwarsa, don haka ba za su bude asusun ajiyarsa ba, har sai ya tabbatar musu a “hukumance cewa yana nan a raye.”
Mutum ya fara fuskantar matsala ce bayan da ya je cinikin kayan masarufi, ya mika katinsa na ciniki domin a zari kudin. Sai kawai aka sanar da shi cewa katin ba ya aiki. Nan da nan ya garzaya na’urar ATM don ya ciro kudin, amma katin ya ki aiki.
Mutumin wanda aka sakaya sunansa yana fita daga kantin, sai ya garzaya zuwa banki, don ya sanar da su matsalar katinsa na hada-hadar kudi, sai kawai suka ce an rufe katin cirar kudi da yake amfani da shi, domin an tabbatar da cewa ya mutu, kamar yadda jaridar katar, Al Shark ta ruwaito, a ranar Talatar makon jiya.
Mutumin ya yi ta kokarin nuna cewa yana nan a raye, har ya rika daga muryarsa, yana karaji amma ma’aikatan bankin suka ki amincewa da shi, suka kuma jajirce cewa sai ya gabatar da takardar shaidar hukuma da za ta nuna cewa yana raye, kafin su bude asusun ajiyarsa.
Matakin farko da ya kamata ya dauka, shi ne ya kawo shaidar hukuma. Don haka ya tuntubi Hukumar Lafiya ta kasar, sai kawai aka aiko masa da shaidar mutuwarsa, kamar yadda jaridar ta bayyana.
Mutumin ya rankaya zuwa Hukumar Jin Koke-Koken Jama’a, inda ya kai karar hukumar lafiyar, ya bukaci ta kawo hujjojin da ke nuna cewa ya mutu. Ya ce mai yiwuwa wajen shigar da bayanan wani ne ta yi kuskuren sanya masa “mutuwa.”
A halin yanzu dai mutumin ya dauki lauya don taimaka masa a warware matsalar.
Lauyan mai suna Falah Al Mutairi, ya bayyana wa jaridar Al Shark, cewa “Irin wannan takaddamar shari’a ba kasafai takan kasance ba. Ina da tabbacin cewa an yi kuskure ne wajen saka sunan wani da bayanansa da suka kusa zama iri guda. Amma ni ban ga wani dalili da zai sa a yi hakan ba, domin babu wani rudani. Za mu tabbatar musu da cewa wanda nake karewa yana nan a raye, kuma sai mun tabbatar an bude masa asusun ajiyarsa; kuma a shafe wadancan hujjoji da ke nuna cewa ya mutu.”