Aminiyar Kurmi• Created August 19, 2022 07:15
Ya je daukar mahaifiyarsa cikin gawarwakin da matsafa suka busar a Edo
’Yan sanda na tsaka da bincike a wurin da suka kama ‘mastafan’ da busassun gawarwakin mutumin ya isa wurin, cewa ya zo daukar gawar mahaifiyarsa domin yin bikin jana’izarta
Takaddama ta barke bayan wani mutum ya je daukar gawar mahaifiyarsa a cikin gawarwaki 20 da ake zargi matsafa su busar a Jihar Edo.
Tun da farko ’yan sanda sun kama wasu mutane da ake zargi mastafa ne, da busassun gawarwakin mutane a cikin wani kango a Benin, hedikwatar Jihar Edo.
’Yan sanda na tsaka da gudanar da bincike a wurin da suka kama ‘mastafan’ da busassun gawarwakin mutumin ya isa wurin, cewa ya zo daukar gawar mahaifiyarsa domin yin bikin jana’izarta.
A cewar mutumin, ya kai gawar mahaifiyar tasa dakin ajiyar gawa ne saboda a lokacin da ta rasu a 2021 ba shi da kudin gudanar da hidindimun jana’iza — yana so sai ya tara kudade ya shirya mata gagarumin bikin jana’iza.
Kakakin ’yan sandan Jihar Edo, SP Chidi Nwabuzor ya ce mutumin ya shaida musu cewa, “Mai wurin, wanda sunansa Chukwu Otu, wanda yanzu ya tsere yana gudanar da wani dakin ajiyar gawa ne a garin Benin.”
Chibuzor ya ce bayan rasuwar dattijuwar a wani asibiti a Uselu a 2021, sai danta ya kai gawarta a ajiye sai ya samu kudi ya shirya mata bikin jana’izar kasaita.
“Yanzu da ya samu kudin sai ya je inda ya kai gawar, amma aka ce masa Chukwu Otu ya tashi daga nan ya koma Ekenwan Road, unguwar Asoro area, Uzebu Quarters.
“Da ya zo wurin sai suka bukaci ya kawo katin shaidar ajiyar gawar, amma a lokacin bai je da katin nasa ba.
“Shi ne suka ce ya za da katin wata rana, shi ya sa ya dawo, yanzu ya gabatar da katin, wanda yanzu yake hannun ’yan sanda,” in ji kakakin ’yan sanda.
Ya kuma bayyana cewa Chukwu Otu ya tsere, amma an yi nasarar cafke wasu mutum hudu kuma suna taimaka wa ’yan sanda a binciken da ake gudanarwa.
Sai dai daya daga cikin wadanda ake tsare da su ya nesanta kansa da zargin ayyukan tsafi.
A cewarsa, zuwa wurin ya yi domin bincikawa ko ya samu aikin tuki da ya nema.
“Da na je ina neman daraktan wurin sai mutanen unguwar suka hau ni da duka, suka kai ni ofishin ’yan sanda, ba tare da sun saurare ni ba.
Amma, SP Nwabuzor ya bayyana cewa babu yadda za a yi wurin ya zama dakin ajiyar gawa, alhali babu wata alama ko allon shaida da ke nuna haka.
Uwa uba wurin ya fi kama da inda ake tsubbace-tsubbace, ganin yadda aka zuzzuba jinin dabbobi.