Ya je Maiduguri daga Legas a kan keke

Ya kammala balaguronsa a kan keken daga Legas zuwa Maiduguri a cikin kwanaki 8 kacal.

Ya je Maiduguri daga Legas a kan keke

Wani mahayin keken hawa, Samuel Fastuma, ɗan asalin Jihar Benue, ya kammala balaguronsa a kan keken hawa daga Legas zuwa Maiduguri, babban birnin Jihar Borno a cikin kwanaki 8 kacal.

A cewar Fastuma, ya fara wannan tafiya ce a ranar Lahadi 19 ga watan Janairu, 2025 bisa ƙudirinsa na nuna fatan alheri ga daukacin masu yaƙi da fatara da masu yaƙi da muggan ƙwayoyi da kuma neman hadtin kai da zaman lafiya a tsakanin al’ummar Nijeriya.

Da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan isar sa birnin na Maiduguri, Fastuma ya ce, ya fara wannan tafiya ce domin yi wa matasa fatan alheri da kuma yin kira da a zauna lafiya a tsakanin ’yan Nijeriya.

Fastuma ya ce, “ina so in sanar da matasa, cewa abubuwa za su daidaita a cikin kasar nan don haka a cigaba da sa rai a kan hakan.

“Na yi imani cewa, idan kuna da basira, ya kamata ku yi amfani da ita domin hakan kan iya haifar da abubuwa masu girma na ci gaba.

“Tafiyar da na yi ta tsawon kwana takwas, na hadu da kalubale da dama da suka hada da rashin kyawun hanyoyin mota a wasu yankunan.”

Fastuma ya ce, “akwai wasu wurare masu kalubale, musamman tsakanin Bida da Npai, inda titin ba shi da kyau sosai.

“Haka nan na kuma fuskanci wasu matsaloli na bin hanyar Kano zuwa Potiskum.”

Duk da wadannan kalubale Fastuma ya jajirce kuma ya samu nasarar isa Maiduguri a ranar 26 ga watan Janairu.

“Na sha jin labarin Jihar Borno, amma wannan shi ne karo na farko da na kawo ziyara,” in ji shi.

‘‘Tsaro a kan titin ya yi matukar tsauri, kuma ya zuwa yanzu, na gano Jihar Borno wuri ne mai dadin rayuwa.”

Tafiya ta ban mamaki irin ta Fastuma tana zama abin sha’awa ga al’umma, musamman lura da halin matsalar tsaro da wasu yankunan kasa ke ciki.