Ya kafa sabuwar bajinta wajen buga rubutun kwamfuta da hanci

Zakaran buga rubutun kwamfuta da hanci na duniya Mohammed Khurshid Hussain ya kafa sabuwar bajinta wajen sauri yayin buga rubutu da hancinsa. Khurshid Hussain, mai shekara 23, dan kasar Indiya ya rubuta bakake 103 da hancinsa cikin dakika 47 bayan ya ba kansa horo na awa shida a kullum, kamar yadda jaridar International Business Times ta […]

Ya kafa sabuwar bajinta wajen buga rubutun kwamfuta da hanci

Zakaran buga rubutun kwamfuta da hanci na duniya Mohammed Khurshid Hussain ya kafa sabuwar bajinta wajen sauri yayin buga rubutu da hancinsa.
 Khurshid Hussain, mai shekara 23, dan kasar Indiya ya rubuta bakake 103 da hancinsa cikin dakika 47 bayan ya ba kansa horo na awa shida a kullum, kamar yadda jaridar International Business Times ta ruwaito.
Idan aka tabbatar da haka, ya rusa bajintar baya ta rubuta wannan adadi a cikin minti daya da dakika 33 da wani dan kasar Indiya ya kafa a Dubai a shekarar 2008, wanda shi ya yi amfani da hancinsa wajen rubuta adadin wannan jumla: “Kundin Tarihi na Duniya ne ya kalubalance ni in buga wannan jimla ta amfani da harshena cikin sauri”. Inji Khurshid Hussain.
Malam Hussaini, wanda ya fito daga kudancin birnin Hyderabad ya shafe watanni yana atisaye domin rusa wannan bajinta ta dakika 53, bayan ya cimma haka akalla sau biyu.
A yayin wannan yunkuri, an daure hannuwansa ta baya, kuma dimbin ’yan kallo masu sha’awa da masu wucewa da sauran masu sanya ido suka zuba ido kan maballan buga kwamfutar. Daga baya, an tura hoton bidiyo da bayanan da aka gabatar ga manema labarai a shafinsa na Youtube.
Hussain ne ke rike da kambin rubuta daukacin haruffan Ingilishi cikin sauri – duk da yake an ce ya cimma hakan ne ta hadawa da yatsu, kuma ya buga su ne cikin dakika uku da digo 43 a yayin wani kalubale da ya gudana a Fabrairun 2012 a gaban ’yan jarida da dama a gasar da aka gudanar a jiharsa.
Ya shaida wa jaridar International Business Times cewa: “Idan kana son kafa tarihi kowane digo na dakika abin kirgawa ne. Na buga rubutun ne da idona daya a rufe, kuma yana da wuya ta wata fuskar ka gano maballan.”
Shi ne buga rubutu mafi ban mamaki da littafin tarihin ya taba cin karo da shi.
A bara wani Ba’amurke mai suna Mark Encarnación ya yi amfani da wayar smartphone wajen rubuta jumlar: “The razor-toothed piranhas of the genera Serrasalmus and Pygocentrus are the most ferocious freshwater fish in the world. In reality they seldom attack a human”, a cikin dakika 25 da digo 9 – alhali an daure masa ido.
Sannan akwai tarihin da aka kafa wajen buga lamba ta 1 zuwa ta 50 tare da aya a tsakanin kowace lamba. Kuma Hind Al Mulla, daga Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ce ta samu nasara cikin dakika 16 da digo 37 a gasar da aka gudanar a Dubai a shekarar 2009.
Ba hanci ba ne kawai ake amfani da shi wajen buga rubutu, domin wani mutumin China da ya rasa hannuwansa, mai suna Liu Wei ya buga harrufa 251 a jerin abacada da kafarsa a wani shiri na gidan talabijin na Italiya a shekarar 2010 ba tare da samun kuskure ba.