Ya kai karar mai biko kan neman auren matarsa

Wani magidanci da ke zaune a garin Dakwa da ke karamar Hukumar Bwari a yankin Birnin Tarayya Abuja, ya kai karar makwabtansa biyu a Kotun Yanki ta garin Deidei, Abuja, inda yake zargin daya daga cikinsu da neman auren matarsa. Magidancin Mukhtar Bello wanda da farko ya je kotun a matsayin wanda aka kai kararsa, […]

Ya kai karar mai biko kan neman auren matarsa

Maryam Alooma Mukhtar Babban Jojin NajeriyaWani magidanci da ke zaune a garin Dakwa da ke karamar Hukumar Bwari a yankin Birnin Tarayya Abuja, ya kai karar makwabtansa biyu a Kotun Yanki ta garin Deidei, Abuja, inda yake zargin daya daga cikinsu da neman auren matarsa.
Magidancin Mukhtar Bello wanda da farko ya je kotun a matsayin wanda aka kai kararsa, bayan da matarsa Hauwa’u Sani ta nemi a raba auren da suka yi bayan mako daya da daura shi. Magidancin ya shigar da karar ce bisa zargin cewa ya nemi wani abokinsa mai suna Usman Ibrahim ya yi masa bikon matarsa, shi Usman ya gayyato daya daga cikin wadanda ake karar suka je wurin bikon tare bisa izinin Mukhtar.  Ya ce abokin nasa ya shaida masa cewa, ya janye yunkurin nasa a sakamakon tirjiya da matar ta nuna.
A daya daga cikin zaman kotun, magidancin ya ce, daya daga cikin wadanda yake kara Kabiru Plumber, ya koma wurin matar tare da mutum na biyu da ake zargi mai suna Shu’aibu Ibrahim, inda suka kebance da ita ba tare da yawunsa ba.
Kuma ya ce, daya daga cikin wadanda ake zargin Shua’ibu Ibrahim ya sake komawa wurin matar tasa a gidan magabatanta da ke garin Dakwa a karo na biyu, inda ya kebance da ita na tsawon lokaci.
Da yake amsa tambayar kotun, wanda ake zargin Shu’aibu Ibrahim ya ce ya ziyarci matar ce a bisa radin kansa da nufin sasanta su, kuma sau daya ya je ba sau biyu ba. Sai dai da kotun ta nemi jin ta bakin matar, Hauwa’u Sani ta ce sau biyu ne wanda ake zargin ya ziyarce ta. Sai dai ta ce ziyara ta biyu, ita ce ta gayyace shi, don tattauna mas’alar kudin kul’i da ta yi shawara da shi don mayar wa mijin.
Alkalin Kotun Mai shari’a Jamilu Abdulkadir ya zarge shi da yunkurin boye gaskiya ga kotun, al’amarin da ya bayyana a matsayin laifi, jin haka ke da wuya, sai Shu’aibu ya saki jiki ya fadi sume, inda aka wuce da shi zuwa wani asibiti da ke garin Deide.
A nasa bangaren mutum na biyu da ake zargi, Kabiru Plumber ya ce ya je gidan ne wurin ’yarta, wadda yake nema da aure.  Amma sai Mukhtar Bello ya karyata shi, inda ya ce ya sanar da shi a baya cewa ya janye neman ’yarta saboda wasu dalilai.
Mai Shari’a Jamilu Abdulkadir, ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 24 ga Oktoba sakamakon sumar da daya daga cikin wadanda ake karar ya yi.