Ya kai karar ’yarsa kotu yana neman a kashe aurenta

Wani uba mai suna Abbati Datti Wudil ya gurfanar da ’yarsa a gaban Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Gyadi-Gyadi a birnin Kano yana neman kotun ta kashe auren ’yar da mijinta bisa zargin mijin da kasancewa boka. Abbati Datti Wudil ta bakin lauyansa Bashir Muhamamd ya bayyana wa kotu cewa tun farko ’yarsa ta […]

Ya kai karar ’yarsa kotu yana neman a kashe aurenta
Ya kai karar ’yarsa kotu yana neman a kashe aurenta

Wani uba mai suna Abbati Datti Wudil ya gurfanar da ’yarsa a gaban Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Gyadi-Gyadi a birnin Kano yana neman kotun ta kashe auren ’yar da mijinta bisa zargin mijin da kasancewa boka.

Abbati Datti Wudil ta bakin lauyansa Bashir Muhamamd ya bayyana wa kotu cewa tun farko ’yarsa ta yi aure ne ba bisa yardarsa ba, idan ya ce wata kotun shari’ar Musulunci ce ta daura auren ’yarsa wata uku da suka gabata.
Lauyan mahaifin ya kara da cewa yana son a kashe auren ne saboda bai yarda da sana’ar mijin ’yar tasa ba wanda a cewarsa bincike ya nuna cewa boka ne.
Da take bayani kan da’awar mahaifinta wacce aka yi kara mai suna Sadiya Abbati ta bayyana wa kotu cewa har yanzu tana son mijinta ba kuma za ta rabu da shi ba. Haka kuma ta ce ta gamsu da sana’ar mijinta wanda a cewarta dillalin filaye da gidaje ne.
Da yake mayar da martani kan da’awar ’yarsa mahaifin ya nemi kotu ta jingine auren ’yar zuwa lokacin da za a yanke hukunci, lamarin da kotun ta ki amincewa da shi inda ta ce shari’ar ba za ta dauki tsawon lokaci ana gudanar da ita ba.
Alkalin Kotun Mai shari’a Kabir Imam ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 25 ga watan Maris din nan.
Wacce ake kara Sadiya Abbati wacce a yanzu take mataki na karshe a karatun digirinta ta shaida wa Aminiya cewa tunda farko mahaifinta ya nuna cewa sai ta yi karatu mai zurfi kafin ya aurar da ita. “Da ma ya nuna cewa sai na yi samu digiri na biyu sannan zan yi aure, lamarin da ni kuma na ji ban amince da shi ba, saboda ina son yin aure. To a shekaruna idan ban yi aure ba, so yake yi na yi karuwanci ko kuwa? Hakan ya sa na rika tura masa mazajen da suke neman aurena har sau 12, amma yana korarsu, har mutanen unguwa suka rika zargin ko nemana mahaifina yake yi.”
Ta kara da cewa: “A kan na nuna masa cewa ina son yin aure sai ya saki mahaifiyata saki uku. To bayan na samu wannan mijin nawa na kai masa shi sai ya ki yarda. Hakan ya sa na kai kotu na nemi ta sa shi ya yi min aure a karshe kotun ta daura min aure.”
Sadiya ta ce babu alaka mai kyau tsakaninta da mahaifinta ko danginsa, “domin ko gidan daya matarsa ba mu sani ba shekara tara da aurensu,” inji ta.
Abbati Wudil wanda ma’aikacin Kwastam ne a Legas ya musanta batun ya ce sai ta yi kammala karatu zai yi mata aure, inda ya ce abin da ya sa shi daukar wannan mataki saboda bai gamsu da mazajen da suke neman auren ’yar tasa ba ne. “Ban taba cewa ba za ta yi aure ba, domin na ba wa ’yar uwata har Naira dubu 400 don a saya mata kayan daki. A matsayina na mahaifinta ina kokarin kare mata mutunci wajen zaba mata miji nagari. Domin tana son yin aure ba kowane namiji za ta aura ba, ta yaya za a ce ’yata tana auren boka?,” inji shi.
Bayanai sun ce a watanni baya Sadiya Abbati ta yi karar mahaifinta ga Hukumar Hisba don ta sa mahaifinta ya aura mata mijin da take so, lamarin da Hisbar a karkashin Kwamandanta Sheikh Aminu Daurawa ta kori karar, inda daga nan ta shigar da kara a
Kotuna Shari’ar Musulunci ta Uku da ke cikin birni, a karshe kotun ta daura aure tsakanin Sadiya da kuma angonta Muhamamd Yahaya Wali Maidoki.
Aminiya ta samu labarin cewa kafin kotun a karkashin Mai shari’a Ibrahim Sarki Sani Yola ta daura mata aure ta aika wa mahaifinta sammaci a lokuta da dama amma bai amsa kiran kotun ba, inda daga nan kotun ta yi amfani da damarta ta daura auren.