Ya kai wa ’yan sanda cin hancin N1.5 su sako ɗan Shi’a

Wanda yake so a sako babban dan Shi’a ne mai daukar nauyin ayyukan IMN a Abuja

Ya kai wa ’yan sanda cin hancin N1.5 su sako ɗan Shi’a

’Yan sanda sun kama wani wanda ya kai musu cin hancin Naira miliyan 1.5 domin su sako wani dan Shi’a da suke tsare da shi kan rikicin Kasuwar Wuse da ke Abuja.

A rikicin ’yan Shi’a da ’yan sanda a Kasuwar Wuse ne aka kashe mutane uku ciki har da ’yan sanda biyu, aka jikkata wasu uku, aka  kuma kona motocin ’yan sanda uku.

Wanda aka kama din dan kungiyar ’yan Shi’a ta IMN ne, a cewa Kwamshinan ’yan sandan Abuja, Benneth Igweh.

Igwe ya ce wanda mai bayar da cin hancin ke son a saki babban dan Shi’a ne kuma daya daga cikin masu daukar nauyin ayyukan IMN a Abuja.

Kwamshinan ya ce wanda ake zargin da kuma wanda yake neman a saki din, suna nan suna amsa tambayoyi kafin a gurfanar da su a gaban kuliya.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos