Ya kalubalanci masu dukiyar Arewa kan kafa kafofin watsa labarai

Babban Manajan Gidan Rediyon Jihar Yobe Alhaji Ibrahim Bulama Daciya ya kalubalanci masu dukiya da ke Arewa kan su yunkura don kafa kafofin watsa labarai da za su yi gogayya da na Kudu domin dakile farfagandar da suke yi wajen cin dunduniyar yankin Arewa.Alhaji Ibrahim Bulama Daciya ya bayyana haka ne a tattaunawarsu da Aminiya […]

Ya kalubalanci masu dukiyar Arewa kan kafa kafofin watsa labarai
Ya kalubalanci masu dukiyar Arewa kan kafa kafofin watsa labarai

Babban Manajan Gidan Rediyon Jihar Yobe Alhaji Ibrahim Bulama Daciya ya kalubalanci masu dukiya da ke Arewa kan su yunkura don kafa kafofin watsa labarai da za su yi gogayya da na Kudu domin dakile farfagandar da suke yi wajen cin dunduniyar yankin Arewa.
Alhaji Ibrahim Bulama Daciya ya bayyana haka ne a tattaunawarsu da Aminiya a Damaturu inda ya ce, abin takaici ne yadda masu hannu da shunin da ke Kudu ke bude kafofin watsa labarai don cimma burin yakar Arewa ta yadda a kullum sukan fadi munanan abubuwa kan Arewa da al’ummarta a fannin mulki da tattalin arziki da addini da al’adu, amma masu dukiyar Arewa suke yin barci a wannan fanni.
Alhaji Bulama Daciya ya ce duk da a ’yan shekarun nan an samu wasu masu kishi a Arewa sun bude wasu kafofin watsa labarai musamman jaridu da gidajen rediyo da suke taka rawar gani wajen kare mutuncin Arewa, ya ce in da za a samu irinsu da yawa mutanen Kudu za su shafa wa Arewa lafiya.
Manajan ya koka kan yadda gwamnonin Arewa suka yi biris tare da jan kafa wajen farfado da kamfanin buga jaridun New Nigerian da Gaskiya Ta Fi Kwabo mallakarsu wanda a shekarun baya shi ne yake kokarin kare mutuncin Arewa da al’ummrta.
Ya bukaci gwamnonin Arewa su hanzarta farfado da kamfanin tare da inganta kafofin watsa labarai da suke yankinsu, kuma su da masu hanu da shuni su rika ba da goyon baya ga gidajen watsa labaran ta hanyar ba su tallace-tallace da za su taimaka musu wajen tsayawa da kafafunsu.
Sai ya yaba wa gwamnatin Jihar Yobe a karkashin Gwamna Ibrahim Gaidam kan yadda take kara inganta kafofin watsa labaranta ta hanyar samar musu da kayayyakin aiki na zamani da kula da ma’aikata. Ya bukaci ma’aikatan su saka wa gwamnatin ta wajen kula da aikinsu.