Ya kamata a ɗauki matakin gaggawa kan cin zarafin mata a Najeriya —MDD
Yayin da Najeriya ta bi sahun kasashen duniya wajen bikin kwanaki 16 na fafutukar yaki da cin zarafin mata, Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya, ta yi kira da a dauki matakin gaggawa, a kan cin zarafi mata a kasar.
Yayin da Najeriya ta bi sahun kasashen duniya wajen bikin kwanaki 16 na fafutukar yaki da cin zarafin mata, Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya, ta yi kira da a dauki matakin gaggawa, a kan cin zarafi mata a kasar.
Wakilin MDD a Najeriya Mohammed M. Fall, wanda kuma shi ke kula da ayyukan jin kai ya koka game da alkaluman da ake samu game da cin zarafin mata a duniya da aka fitar inda ya ce daya daga cikin mata uku na duniya na fuskantar cin zarafi a kuma ana cin zarafin mace a kowane minti 10.
Ya ce a Najeriya, kashi 31% na mata daga shekaru 15 zuwa 49 sun fuskanci cin zarafi, a cewar wani rahoto da aka fitar a shekarar 2018 kuma adadin na iya karuwa duba da wadanda ba a bayar da rahotanninsu ba musamman a lokacin annobar COVID-19.
’Yan sanda sun ceci matafiya 20 daga hannun ’yan ta’adda a Katsina
Ya jaddada mahimmancin samar da wurare masu aminci inda mata da ‘ya’ya mata za su iya samun ingantaccen ilimi, aikin yi, kiwon lafiya, da gudanar da rayuwa mai inganci ba tare da fargaba ba. “Babu al’ada ko kabila ko addinin da ya yarda a rika cin zarafin mata a duniya”
Fall ya jaddada cewa ba MDD ba za ta iya samun nasarar wannan fafutukar ita kadai ba inda ya yi kira da a hada kai da shugabannin al’umma da na addini da daidaikun jama’a domin samar da ci gaba a Najeriya.
Juyin mulkin Syria: Iran ta tuntubi wadanda suka kifar da Al Assad
“Aikinmu a Najeriya shi ne mayar da hankali kan inganta rayuwa da samun adalci tare da wayar da kan jama’a don canza musu tunani da ɗabi’a. Amma ba za mu iya cimma hakan mu kadai ba. Muna bukatar gudummuwar kowa.”