‘Duk wanda ya sayi fom din takarar APC N100m a bincike shi’
Abin mamaki ne Buharin da sai da ya ci bashi ya iya sayen fom Naira miliyan 27 a 2014 yanzu ya yarda a kara kudin zuwa Naira miliyan 100
Jam’yyar PDP ta bukaci hukumomin yaki da rashawa su binciki duk dan siyarsar da ya sayi fom din takarar shugaban kasar jam’iyyar APC a kan Naira miliyan 100.
Shugaban Jam’yyar PDP na Kasa, Doktar Iyorchia Ayu, ya ce tsuga kudin fom din takarar shugaban kasar da APC ta yi a kan Naira miliyan 100 alama ce da ke nuna jam’iyyar na shirin ci gaba da jefa ’yan Najeriya cikin mawuyacin hali.
- 2023: ‘Da biyu jam’iyyu suka tsauwala kudin fom din takara’
- 2023: ‘Da biyu jam’iyyu suka tsauwala kudin fom din takara’
“Wannan shi ne kololuwar rashin tunani da ban mamaki kuma duk mutumin da ya sayi fom Naira miliyan 100 ko miliyan 50 ya kamata a bincike shi kan almundahana,” inji sanarwar da kakakinsa, Simon Imobo-Tswam, ya fitar.
Ya bayyana cewa, “Tsuga kudin farashin takardar tsayawa takara a kan Naira miliyan 100 da miliyan 50 da sauran ya fito da munafurcin APC a fili.
“Yanzu ’yan Najeriya sun ga cewa APC ba komai ba ce face hadakar bangarori daban-daban domin su karbi mulki su jefa ’yan Najeriya da ’yan jam’iyyar a matsanancin kunci.”
“’Yan Najeriya na sane da yadda a 2014 Shugaba Buhari kuma shugaban APC, lokacin yana neman takara ya bayyana musu cewa bashin Naira miliyan 27 ya karba don sayen takardar tsayawa takarar shugaban kasa a wancan lokaci.
“Amma yau shi din, a matsayinsa na shugaban jam’iyyar ya yarda a sayar da fom Naira miliyan 100! Karin ya haura kashi 370 cikin 100.
“A 2014, PDP ke kan mulki kuma tattalin arzikin Najeriya yana bunkasa, ba yanzu ba da APC ta gurgunta tattalin arzikin, saboda rashin iya shugabanci, Najeirya ta zama “Hedikwatar Talauci ta Duniya.”
Ya ci gaba da cewa ta “Ina dan APC da aka riga aka talauta zai iya sayen fom a wannan farashi da aka tsawwla? Duk da cewa kwanan nan Buharin ke maganar “Samun Cikakkiyar Dama ga Kowannensu”.
“Da wannan tsuga kudi, APC ta hana dubban matasanta damar shiga siyasa, gami da sanyaya gwiwar dubban matasan Najeriya da suka yaba wa Buhari kan sanya hannu a bias dokar ba wa matasa damar shiga siyasa — Not Too Young To Run, a 2018.”
“Wannan shi ne makurar rashin tunani da ban mamaki, saboda haka wani dan siyasa da ya sayi fom Naira miliyan 100 ko miliyan 50 ya kamata a bincike shi.
“Mu a PDP mun bambanta saboda muna tare da ’yan Najeriya, shi ya sa kudin fom dinmu ke da sauyi domin samar da dimokuradiyya.
“Idan aka kwatanta namu da nasu, bambancin a fili yake, shi ya sa wajibi ne mu karbi mulki domin ceto ’yan Najeriya daga wannan gwamnati mara hangen nesa.”