Ya kamata a ci gaba da kai manyan jami’an gwamnati kasashen ketare don neman magani?

A makon jiya ne wadansu kafafen yada labarai suka ruwaito wani rahoto da yake cewa an fitar da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban kasa Alhaji Abba Kyari kasar waje don nema masa magani. Ga ra’ayoyin jama’a game da yadda suke ganin matakin neman wa manyan jami’an gwamnati magani a kasashen ketare: Bai dace a ci gaba […]

Ya kamata a ci gaba da kai manyan jami’an gwamnati kasashen ketare don neman magani?
Ya kamata a ci gaba da kai manyan jami’an gwamnati kasashen ketare don neman magani?

A makon jiya ne wadansu kafafen yada labarai suka ruwaito wani rahoto da yake cewa an fitar da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban kasa Alhaji Abba Kyari kasar waje don nema masa magani. Ga ra’ayoyin jama’a game da yadda suke ganin matakin neman wa manyan jami’an gwamnati magani a kasashen ketare:

Bai dace a ci gaba ba – Umar Zico

Daga Ahmed Ali, Kafanchan

Umar Zico: “Bai dace a rika fita da su waje ba. Domin ko kasashen da suke zuwa irinsu Amurka da Ingila da Dubai da sauransu sun tsaya sun inganta asibitocinsu ne da kayan aiki na zamani wanda mu ma inda za mu yi hakan da babu maganar fita kasashen waje tun da Allah ya albarkace mu da kwararrun likitoci. Kwanan nan likitocinmu 900 suka yi tururuwa zuwa Abuja don neman aiki a guraben mutum 400 kawai da aka nema, ka ga wannan yana nuna maka akwai kwararrun likitoci a kasar nan tun da ko manyan kasashen waje ka je za ka samu likitocinmu na aiki a can. Abin kunya ne fita kasashen waje don neman magani maimakon haka a tsaya a inganta asibitocinmu na zamani da ingantattun magunguna hakan shi zai fi mana.”

Bai dace su rika fita waje don neman magani ba – Hafsat Idris

Daga Ahmed Ali, Kafanchan

Hafsat Idris: “A ganina bai dace a rika fita da manyan gwamnati zuwa kasashen ketare ba kan wasu cututtuka ba, alhali talakawa da mutanen karkara na ta mutuwa kan kananan cututtuka kan rashin ko rashin kudin zuwa asibiti ba. In da gaske ne batun “Canji ya fara daga kaina” to kamata ya yi mu ga suna amfani da irin magungunan da suke bari a kawo mana kasar, ko ake yinsu a cikin kasar in dai har sun yarda da wanda ake ba mu a asibitocinmu idan ko ba haka ba ka ga babu ranar da za su tsaya su gyara mana namu tun da abinci ma sun fi so mu yi na cikin gida to ya kamata mu yi amfani da likitocinmu da asibitocinmu na gida su ma, in ko ba haka ba babu ranar inganta mana suke nan, ka ga da sauran canji ke nan.”

Ba na goyon bayan ci gaba da kai su kasashen waje
– Anas Ja’en

Daga Abbas dalibi, Legas

Anas Saminu Ja’en: “A gaskiya don nema masu magani domin yin hakan na nuna wa kasashen duniya gazawar kasar mu, kuma ma fi yawa da dukiyar talaka ake amfani, to mai zai hana a yi amfani da wadannan makudan kudin a inganta asibitocin mu wanda talakawa suma za su amfana? Babban abin takaicin shi ne hatta yawancin likitocin da suke aiki a kasashen wajen ‘yan Najeriya saboda gwamnati ta kasa biyan su albashi da rashin kayan aiki na zamani shi ne suka tafi wasu kasashen, ya kamata gwamnati da ma’aikatar lafiya ta kasa su duba wannan batun.”

Bai kamata ba – Malam Aminu

Daga Abbas dalibi, Abeokuata

Malam Aminu Ya’u: “Bai kamata a ce ana fitar da manyan jami’an gwamnati kasashen waje ba don neman masu magani, idan asibitocin mu na gida ake kai su anan ne za su san halin da asibitocin namu suke ciki, za su gane wa idanuwansu irin tabarbarewar yanayi da halin gyara da daukin da suke bukata, ta haka ne za a samu bai wa asibitocinmu cikakken kulawa amma muddin ana fitar da manya waje a haka namu cibiyoyin kiwon lafiyar za su ci gaba da tabarbarewa, don haka muna fatan ganin ire-iren wannan sauyi da wannan sabuwar gwamnatin ta yi ta ikirari a baya.”

Bai dace ba a ci gaba ba
– Alhaji Sani

Daga Jabiru A Hassan, Kano

Alhaji Sani Kirya: “Yana da kyau a rage kudin da ake kashewa a wasu ayyuka domin yin amfani da su wajen kyautata asibitocin kasar nan, domin wasu lokutan ana ware kudi domin gudanar da wasu ayyuka wadanda ko kadan ba su da amfani sosai ga al’umma ta kowane fanni. Ana kashe manyan kudade wajen fitar da manyan mutane zuwa asibitoci na kasashen waje saboda babu ingantattun asibitoci a kasa. Kuma ba za a iya hana kowa fita ba tun da guraren kula da lafiya da ake da su a kasarnan ba su da yanayin da kowa zai tsaya neman magani. Saboda haka wajibi ne gwamnatoci su mayar da hankalin su wajen inganta asibitocin.”

Ba na goyon bayan ci gaba da fita da su – Malam Yusha’u

Daga Jabiru A Hassan, Kano

Malam Yusha’u Ahli: “Ni a ganina idan aka inganta asibitocin da ke kasarnan ko shakka babu kowa zai tsaya a gida ya nemi magani ba tare da an fita kasashen waje ba. Kowa dai ya san cewa Allah Ya ba mu kwararrun likitoci da kuma karfin tattalin arzikin arzikin kasa wanda za a iya kyautata yanayin asibitocinmu ta yadda kowa zai je neman magani. Maimakon kashe makudan kudade wajen tafiya waje domin su ma inda ake tafiya din tsayawa suka yi suka inganta asibitocin su domin kula da lafiyar al’umomin su sabanin yadda abin yake mu a Najeriya. Don haka ina mai fatan cewa nan gaba kadan gwamnatin tarayya da ta jihohin kasarnan za su himmatu wajen gyaran asibitoci da samar da wadatattun kayan aiki ta yadda za a magance yawaitar fita kasashen duniya neman magani maimakon a tsaya a gida.”