Ya Kamata A Hanzarta Aikin Hako Man Kolmani —Mai Shari’a Pindiga

Mai Shari’a Pindiga ya nuna damuwa bisa jinkirin aikin hako man Kolmani, da cewa kammala aikin zai zama babbar dama ga tattalin arzikin ƙasa

Ya Kamata A Hanzarta Aikin Hako Man Kolmani —Mai Shari’a Pindiga

Rijiyar mai ta Kolmani ce ta farko da samu danyen mai da ya kai na kasuwanci a Arewa maso Gabashin Najeriya. (Hoto: Aminiya/Simon Sunday).

Tsohon Babban Alkalin Jihar Gombe, Mai Shari’a Mu’azu Abdulkadir Pindiga, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta hanzarta aikin hako mai na Kolmani da ke yankin masarautar Pindiga a jihar, da wani ɓangare na Jihar Bauchi. 

Mai Shari’a Pindiga ya nuna damuwarsa kan jinkirin da ake samu wajen ci gaban aikin, inda ya bayyana cewa kammala aikin zai zama wata babbar dama ga tattalin arzikin ƙasa.

Ya ce, “Wannan aiki yana da muhimmanci ƙwarai, kuma idan an kammala shi, zai kasance ginshikin tattalin arzikin ƙasa na dogon lokaci.”

A wata hira da ya yi da manema labarai a Gombe, Mai Shari’a Pindiga ya jaddada cewa aikin man Kolmani zai taimaka wajen haɓaka tattalin arziki ta hanyar ƙara kuɗaɗen shiga da samar da ayyukan yi ga ɗumbin ’yan ƙasa.

“Aikin ba ya buƙatar jinkiri, domin fa’idarsa za ta kasance mai yawa ga ƙasa,” in ji Mai Shari’a Pindiga.

Duk da jinkirin da ake fuskanta, tsohon alkalin ya bayyana cewa yana da kyakkyawan fata cewa Shugaba Bola Tinubu zai ci gaba da aiwatar da wannan “babban aiki,” musamman bayan ganawar da Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya yi da shugaban ƙasa kwanan nan domin tattauna ci gaban aikin hako mai na Kolmani.

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda

An saki matar Ekweremadu daga gidan yari a Birtaniya, ta dawo Najeriya

Trump ya bayar da umarnin kamen ’yan gudun hijira a Amurka