Ya kamata a kira taron makomar kasar nan
Masu karatu ina yi wa dukkan `yan kasar nan murnar zagayowar ranar da kasar nan ta samu `yancin kai, wato cikar shekaru 53 daga Turwan mulkin mallaka na kasar Birtaniya. Bikin bana da aka yi a ranar Talatar wannan makon wato 1 ga watan Oktoba 2013, ana gudanar da shi ne a cikin rudani iri-iri, […]
Masu karatu ina yi wa dukkan `yan kasar nan murnar zagayowar ranar da kasar nan ta samu `yancin kai, wato cikar shekaru 53 daga Turwan mulkin mallaka na kasar Birtaniya. Bikin bana da aka yi a ranar Talatar wannan makon wato 1 ga watan Oktoba 2013, ana gudanar da shi ne a cikin rudani iri-iri, wadanda suka hada da makomar neman takarar tsayawar shugaban kasa, Dokta Goodluck Jonathan a zaben shekarar 2015, da kuma kasancewa babi 2014, in Allah Ya kaimu ita ce shekarar da kasar nan za ta cika shekara 100, cif-cif da hadewar da Turawan mulkin mallaka suka yi wa Arewaci da Kudancin kasar a zaman kasa daya da a yau ake kira Najeriya. Shekarar da aka ce za a iya duba yarjejeniyar zamantakewar kasar nan wala-alla a ci gaba da zaman tare ko kuma a rabu.
Kodayake mai karatu ba akan zagayowar ranar samun `yancin kan kasar nan nike son yin tsokaci a wannan makon ba, aniyata in duba irin cece-kucen da ake ta yi cikin kasa akan a kiran taron kasa don neman makomar kasar nan baki daya, kiraye-kirayen da nike ganin ana ta yinsu ne, don kawai hayaniyar “Kakar” zaben 2015, ta fara kadawa, musamman a cikin jam`iyyar PDP mai mulki da gwamnatin tsakiya tunda akafara mulkin demokradiyya a shekarar 1999.
Kusan makonni biyu da Majalisar Dattawa ta dawo daga hutu, an ji shugaban Majalisar Sanata Dabid Mark a cikin jawabinsa na maraba ga takwarorinsa, yana kiran a yi taron kasa. Shi ma Shugaba Jonathan an ruwaito lokacin da yake karbar rahoton Kwamitin `yan kishin kasa da ke karkashin shugabancin Furfesa Ben Nwabueze, rahoton da ya bada shawarar a kira taron kasa, amma na dukkan kabilun kasar nan, cewa gwamnatinsa ba ta da suka akan a kira taron kasar. Wasu `yan kasa masu fada aji da suka shiga cikin jerin masu kira da a yi taron zuwa yanzu sun hada da tsohon mataimakin shugaban kasar nan, Dokta Aled Ekwueme da tsohon Ministan Yada Labarai, kuma shugaban`yan kabilar Ijaw (kabilar shugaba Jonathan), Cif Edwin Clark da tsohon Gwamnan tsohuwar Jihar Kaduna, Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa.
Taron makomar kasa iri uku ake maganar lallai a dauki daya, akwai masu son a yi taron makomar kasa da zai dage tsarin mulki ya dakatar da dukkan wani zababbe daga kan mukaminsa tun daga kan Kansila zuwa shugaban kasa da mataimakinsa, kama ya zuwa kan `yan Majalisun Dokoki na jihohi da na tarayya baki daya. A takaicen takaitawa a karkashin irin wannan tsarin taro, iko baki daya zai koma hannun shugabannin taron, kowa kuma ya san irin wannan tsari zai yi matukar aiwatarwa a irin wannan lokaci a kasar nan tunda dai ba yaki muka shiga ba (Allah Ya kiyashe mu da yaki).
Tsarin taron kasar na biyu da wasu suke begen a kira, shi ne, wanda zai kasance taron dukkan manya da kananan kabilun kasar nan, wato ma`ana ya kunshi dukkan wakilan kabilun kasar nan sama da 600, da ake da su, shi ma wannan mai karatu idan ka duba za ka ga mahalarta taron sun yi yawa, ta yadda za a iya kammala shi, wasu ma ba su san abin da aka yi ba, bare kuma su gabatar da abin da yake addabar kabilarsu. Tsarin taro na uku da wasu suke bukatar a yi, shi ne ta hanyar zabo wakilan jama`ar kasar nan daga kowane sashe da kungiyoyi, kamar yadda aka saba yi a lokacin taron rubuta kundin tsarin mulki. Wannan tsarin taro na karshe, shi mutane suke ganin zai fi dacewa, mudidn za a yi taron. Amma kuma a gefe daya su kuma `yan Majalisun Dokoki na kasa da na jihohi suna ganin taro kowane iri da sunan makomar kasa, tamfar wani ci baya ne garesu, a zamansu na zababbun wakilan al`umma.
Tabbas fadi batawa, a ce ma kasar nan da al`ummarta suna fama da matsaloli iri-iri, wadanda makasudinsu bai wuce rashin adalcin masu mulki ba, musamman na wannan zamani, wanda yake haddasa kabilanci da gaba da kiyayya a wasu lokutan ma har yakan zame rikici mai kama da kabilanci da addini a kullum tsakankanin mutanen kasa. A yau ta kai inda duk wani ya yi magnar gyaran kasa, kafin a yi nazari akan muhimmancin abinda ya ce, sai an fara fassara shi da kabilarsa ko addininsa ko jinsin da ya fito, wato dan Arewa ne ko Kudu; wane gari ya fito, kuma wane kabila ne? Duk hakan na faruwa ne akan rashin adalcin shugabanni.
Duk wadannan kiraye-kiraye da ake, batun zaben 2015, shi ya bijiro da su, taron da akasarin masu son a yi shi `yan Kudancin kasar nan ne, wadanda a kullum suke daukar Arewa da mutanenta tamfar kansa akan arzikin kasar nan, don wai Arewa ba ta da arzikin man fetur. Haka `yan kudu suka yi ta irin wadannan kiraye-kiraye tun a shekarar 2007, bayan sun fahimci batun“TAZARCE” ta shugaba Obasanjo ta kare.
Wannan hali ake ciki yanzu, ganin takarar shugaba Jonathan tana rawa, shi ya sa shi da kansa da magoya bayansa suke ta kiraye-kirayen lallai sai a taron makomar kasa, don a bajeta a faifai. A ra`ayina, ina ga lokaci ya da `yan Arewa za su ba bori kai ya hau a yi wannan taro, su kuma zama cikin shirin idan an je taron an yanke shawarar a raba kasar nan, to su goyi bayan araba din. Me Arewa ta rasa, da har za ta ji tsoron a raba kasar nan? Arewa ke da yawan al`ummar kasa. Arewa ke da yawan kasar noma rani da damina mai yabanya da dabbobi da duk wani abu na albarkatun kasa fiye da sauran sassan kasar nan, kuma kowa ya sa ni cewa kasashen duniya da suka ci gaba, sun ci gaba ne bisa ga arzikin noma da kiwo.
A nahiyar Afirka akwai kasashe da dama irinsu makwabciyarmu Jamhuriyar Nijar da ba su da arzikin da Arewa take da shi, amma suna rayuwa irin wadda ta fi tamu dadi a yau. Ai kowa ya sa ni a kasar nan kafin a samu arzikin man fetur da arzikin gyada da auduga da kwara da danko da fatu da kira gada ake samu a Arewa, aka kafa harsashin duk wani ci gaba na kasar nan . Don an raba sai me? Ko gobe a kira taron kasa.Shugabanninmu kuma su yarda a raba in ta kama.