Ya kamata a koma koyarwa cikin harsunan Nijeriya — Masana

An zaburar da gwamnati kan ƙudurinta ta na fara aiki da harsunan cikin gida wajen koyo da koyarwa.

Ya kamata a koma koyarwa cikin harsunan Nijeriya — Masana

An zaburar da gwamnati kan ƙudurinta ta na fara aiki da harsunan cikin gida wajen koyo da koyarwa.

Mahalartar taro a kan harsunan Afirka da Jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria ta shirya sun kara tunasar da gwamnati a kan ƙudurinta na amfani da harsunan cikin gida wajen koyar da dalibai a makarantun Nijeriya.

Taron mai taken “Yadda za a bunƙasa harsunan Afirka don samar da ci-gaban ƙasa” ya tattaro masana harsuna daban-daban daga sassan ƙasar.

Farfesa Ahmed Halliru Amfani, malami a Jami’ar Usmanu Danfodio da ke Sakkwato ya nuna muhimmancin yin amfani da harsunan cikin gida don sauƙaƙa fahimtar ɗalibai tare da haɓaka ci-gaban ƙasa.

Sai dai kuma ya sanar da cewa duk harshen da za a yi amfani da shi dole sai ya kasance yana da cikkakken tsari da tasiri a wajen al’umma.

Fafesa Amfani ya ce dole irin waɗannan yarurruka su kasance suna da nagartaccen tsarin rubutu da isassun kalmomi da kuma tsare-tsare da suke alamta cikin kowane harshen a duniya.

Farfesa Bello Alhassan na Sashen Harsunan Afirka wanda ya gabatar da muƙala a taron, ya jawo hankali tare nunar da hanyoyin bunƙasa harsunan ƙasashen Afirka saɓanin amfanin da hanyoyin baya da suka tsufa wajen amfani da su.

Farfesa Alhassan ya ce lokaci ya yi da za a tashi a kan turbar da ake amfani da ita na shekaru aru-aru don samar da sauƙaƙƙiyar hanyar amfani da harsunan Afirka don gina ƙasa.

Ya yi nunu da cewa a baya can dole ne sai ɗalibi ya koyi wani harshe na daban wanda ba nashi ba kafin a koya mishi karatu, inda ya ce hakan ba ƙaramin koma baya ya haifar ba a harkar koyo da koyarwa a makarantu.

Alhassan kuma yi kira da a faɗaɗa fassara kalmomi daban-daban daga wasu yarurruka don bunƙasa harshen Hausa.

Farfesa Aliyah Adamu Ahmed, malama a Jami’ar Jihar Sakkwato ta ce dole ne harshen Hausa ya yi ƙoƙarin haɗiye wasu kalmomi daga yarurruka mabanbanta domin faɗaɗa shi.

Ta kuma yi magana a kan kokarin masana wajen fassara wasu kalmomin turanci musamman na ɓangaren kimiyya don saukaka wa dalibai saurin fahimta.

Farfesa Shuaibu Hassan, Shugaban Sashen Harsunan Afirka na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria ya nuna jin dadin shi bisa amsa kiran da masana harsuna suka yi ga taron.

Ya ce hakan na alamta samun mafita daga halin da harsuna ke ciki ta fuskar inganci da bunƙasarsu.

Ana shi jawabin, shugaban kwamitin shirya taron, Farfesa Kargi, ya ce an samu halarta masana daga jami’oi da yawa inda za a gabatar da muƙaloli sama da 100 a wajen taron.

Yace babban burin taron shi ne samar da mafita kan abubuwan da ke wa harsunan kasashen Afrika tarnaki ta fuskar bunkasa, tare da lalubo hanyoyin bunkasa su don samar da ci-gaban ƙasa.

Cutar Anthrax ta ɓarke a Zamfara

Faston da ke yi wa ’yarsa fyaɗe tsawon shekaru ya shiga hannu

Trump ya rattaba hannu kan gomman dokokin zartarwa

Ƙungiya ta buƙaci rage harajin cinikayya saboda ƙuncin rayuwa