A kori Minista da mashawarcin Buhari kan tsaro —’Yan Majalisa
Mambobin Majalisa sun bukaci Ministan Tsaro, Bashir Magashi da Mashawarcin Shugaban Kasa Kan Tsaro, Babagana Monguno su sauka daga mukamansu
Mambobin Majalisar Wakilai sun bukaci Mai Ba Wa Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaro, Janar Babagana Monguna (Ritaya), da Ministan Tsaro Bashir Salihi Magashi su sauka daga mukaminsa, saboda gaza magance matsalar tsaro da ke addabar Najeriya.
Da suke bayyana bacin ransu kan matsalar tsaron da ta yi wa kasar katutu, ’yan majalisar sun bukaci a dauki kwararan matakai, ciki har da sallamar duk mutanen da ke da alhakin samar da tsaro a kasar, amma suka gaza.
- Yadda mahara suka sace daliban kwalejin lafiya a mahaifar Kwamishinan Tsaron Zamfara
- Yadda aka kama jami’an tsaro za su kai wa ’yan bindiga N60m
A zaman Majalisar a ranar Laraba, Hon. Usman Bello Kumo ya bukaci Shugaba Buhari ya sallami Monguno da Magashi saboda sun kasa yin aikin da aka dora musu.
Hon. Usman Kumo ya bayyana mamakinsa kan yadda Buhari ya ci gaba da aiki tare da Monguno a matsayin mai ba shi shawara kan tsaro, duk da cewa ya gaza kawo kyakkyawan sauyi a yanayin tsaron da Najeriya ke ciki.
Ya bayyana haka ne bayan dan Majalisa Yusuf Gagdi daga Jihar Filato da kuma John Dyegh daga Jihar Binuwai sun gabatar da kudurin kan hare-haren da ’yan bindiga suka kai tare da kashe mutane a kauyuka daban-daban a jihohinsu.
Gagdi ya yi zargin cewa da gangan aka bari mahara suka kai farmakin na Jihar Filato, saboda a cewarsa, an samu kishin-kishin game da farmakin, aka kuma sanar da jami’an tsaro amma suka ki daukar matakin dakile harin.
A cewarsa, baya ga gidaje da wuraren kasuwanci da aka lalata ko aka kona a harin, akalla mutum 3,000 ne aka raba da muhallansu.
Don haka ya bukaci a dauki tsauraran matakai a kan maharan, su kuma jami’an tsaro a tabbata an hukunta su kan sakacin da suka yi wajen kare rayuka da dukiyoyin mutanen Najeriya.
Shi ma da yake tofa albarkacin bakinsa, Hon. John Dyegh ya bayyana cewa an kashe mutum 19 a wasu kauyuka biyu a ranar Litinin da safiyar Talata a Jihar Binuwai.
Dan majalisar ya ce karuwar hare-haren abin damuwa ne musamman ganin yadda jihar take fama da rikice-rikice.
Da yake tsokacinsa, Hon. Benjamin Ben Mzondu ya zargin gwamnati da gaza kare rayuka da dukiyoyin mutanen Binuwai, inda ya ce shugabanni sun gaji da zub da hawaye.