Ya kamata a kori shugaban INEC —Obasanjo
Tsohon shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo, ya bukaci a kori Shugaban Hukumar Zabe ta Kasar (INEC) Farfesa Mahmood Yakubu da wasu manyan jami’an hukumar daga aiki.
Tsohon shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo, ya bukaci a kori Shugaban Hukumar Zabe ta Kasar (INEC) Farfesa Mahmood Yakubu daga aiki.
Obasanjo ya kuma ba da shawarar a sallami wasu manyan jami’an INEC aiki, yana mai kira da a rage tsawon wa’adin shugabancin shugaban hukumar.
Ya yi wannan kira ne a lokcin da yake tsokaci k an zaben shugaban kasa na 2023, wanda ya bayyana mastayin abin takaici.
Don haka ya ba da shawarar a yi cikakken garambawul ga tsarin yadda ake gadanar da zaben kasar.
- Yadda jiragen yaƙi suka halaka ’yan ta’adda a Zamfara
- Zaɓen Ondo: Wanda bai gamsu ba ya garzaya kotu — Tinubu
Ya yi wannan kira ne a lokacin da yake jawabi a taron Zauren Shugabanci na Chinuwa Achebe da ke Jami’ar Yale a kasar Amurka.