Ya kamata a kyale mutane su fara rike bindigu don kare kansu – Gwamnan Katsina

Ya ce yadda ‘yan bindiga ke sayen makaman, ya kamata jama’a ma a ba su dama

Ya kamata a kyale mutane su fara rike bindigu don kare kansu – Gwamnan Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Radda

Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya ce ya kamata gwamnati ta fara kyale jama’a su mallaki bindigu samfurin AK-47 da RPG domin kare kansu kamar yadda ’yan bindiga ke dauka.

Gwamnan ya kuma yi zargin cewa ’yan bindigar na sayen bindigar kai tsaye a kasuwa babu wata doka.

Ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawarsa da ’yan jarida a Abuja ranar Juma’a, inda ya ce sha alwashin cewa gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin bayan ’yan bindigar a Jiharsa.

A cewar Gwamnan, bai kamata a zargi Gwamnoni da gazawa wajen dakile matsalolin tsaro a jihohinsu ba duk da ana cewa su ne manyan jami’an tsaro na jihohinsu amma ba su da damar ba jami’an tsaro umarni.

Gwamnan ya kuma ce yanzu haka gwamnatinsa na can tana tuhumar wasu masu rike da sarautun gargajiya kan zarginsu da alaka da ’yan bindiga, inda ya ce duk wanda suka samu da hannu ba za su kyale shi ba.

Ya ce, “Dole mu yi amfani da mutane wajen kare yankunansu, kamar yadda aka yi da ’yan banda na CJTF a Jihar Borno. Duk lokacin da za su fita aiki za a hada su da jami’an tsaro domin su yi musu rakiya.

“Muna nemna gwamnati ta yi wa dokokin gyaran fuska ta wannan bangaren. Idan dan bindiga zai iya shiga kasuwa kan shi tsaye ya sayi makamai irin su bindigar AK-47 da RPG, ina laifin mutanen kuma da za su kare kansu?

“Su ma ya kamata a ba su damar yin hakan, wadannan mutanen na rike ta ne ta haramtacciyar hanya, mu kuma muna so mu fara rike ta ta halastacciyar hanya. Me ya sa gwamnati ba za ta kyale jama’a su ma su rike ta ba domin kare kansu?

“Sannan ni ban yadda da batun tattaunawa da ’yan bindiga ba, sai dai idan ni zai amfana. Idan dan bindiga ya fito ya ce yana so a tattauna ya ajiye makamai, za mu iya amincewa mu sake karbarsu a cikin jama’a.

“Amma ba zan taba zuwa na roke su su zo mu tattauna da su ba sai dai idan su suka bukaci haka. Idan sun amince sun nemi afiwa, za mu iya yafe musu, ai ’yan uwanmu ne. Amma ba zai yiwu mu je muna ba dan ta’adda kariya ba,” in ji Gwamna Radda.