Ya kamata a mai da hankali sosai ga noma – Manoman Auguda

Aminiya ta tattauna da Alhaji Abdulmumini Muhammad Jega, Shugaban Kungiyar Manoman Auduga ta Jihar Kebbi, babban manomi ne tun zamanin Turawa, ya bayyana gudunmawar da noma ya bayar ga tattalin arzikin Najeriya: A matsayinka na masanin harkar noma wasu dabarun noma ake amfani da su? Kafin zuwan Turawa kakanninmu ba su dogara a kan komai […]

Ya kamata a mai da hankali sosai ga noma – Manoman Auguda

Alhaji Abdulmumini Muhammad Jega Shugaban Qungiyar Manoman Auduga ta Jihar Kebbi

Aminiya ta tattauna da Alhaji Abdulmumini Muhammad Jega, Shugaban Kungiyar Manoman Auduga ta Jihar Kebbi, babban manomi ne tun zamanin Turawa, ya bayyana gudunmawar da noma ya bayar ga tattalin arzikin Najeriya:

A matsayinka na masanin harkar noma wasu dabarun noma ake amfani da su?

Kafin zuwan Turawa kakanninmu ba su dogara a kan komai ba, sai noma, inda suke amfani da takin gargajiya, babu maganin kashe kwari, babu taraktocin noma. Idan sun noma amfanin gonarsu, babu motocin sufuri, sai dai basira irin tasu. Amma yanzu kasar noma ta samu illa, sanadiyyar sinadarin da ake sanya mata, wanda hakan ke haddasa mutuwar wasu halittu da ke taimaka wa kasar, wajen samar da amfanin gona mai yawa.

Najeriya da sauran kasashen Afirka ta Yamma, musamman Arewacin Najeriya sun samu kudade masu yawa wajen sayar da gyada da auduga bayan zuwan Turawa, wadanda da su aka nemo tare da hako man fetur a Kudancin Najeriya da yanzu aka samu wadansu marasa kishin kasa suna farfasa bututun man, suna garkuwa da jama’a da sunan tsagerun Neja-Delta.

Me ya sa noma ya samu koma-baya?

Abin da ya kara kashe aikin noma, idan ka je kauye za ka yi noma, jama’ar wannan kauyen gani suke yi kamar ka zo da kudi ne tunda daga birni ka taho, don haka farashin filin da za a ba mutum ya yi noma daban yake.

Wani abin damuwa shi ne, idan ka ba mutanen kauye kwadago, sai su kwashe amfanin gonar, ya zama ka kashe kudi mai yawa kuma uwar kudin ba ta samu ba, balle a yi batun riba. Don haka, in wata shekara ta zagayo, ba za ka sake sha’awar yin noma ba. Wannan kuma yana kawo wa harkar noma koma-baya sosai.

Wadanne matsaloli ne shugabanni suke jefa noma?

Wadansu shugabanni da suka gabata sun jefa noma cikin matsloli masu yawa, saboda a kullum ana jin gwamnati na cewa ta ware biliyoyin Naira domin sayo taki, a karshe wadanda ba manoma ba ne ke amfana da takin. Kuma ko bashin noma gwamnati ta ba da; za ka ga kashi 65 cikin 100 ba manoma za a ba ba sai dai mai uwa a bakin murhu. Ta yaya za a samu ingantuwar noma a kasar nan, alhali ana hada mutum bakwai a ba su buhun taki daya; amma a ba wani mai hannu da shuni sama da buhu dubu shi kuwa manomin gaskiya bai samu ko buhu biyu ba. A wani lokaci, ko ganin takin wadansu masu uwa a bakin murhu ba sa bari a yi, sai dai a ba su takarda su sayar wa ’yan kasuwa, su kuma su sanya kudinsu aljihu. Amma da yarda Allah irin wannan ta kau, saboda yanzu mun samu Shugaban Kasa, wanda ya kula da harkar noma, kuma batun ka yi sama-da-fadi da takin gwamnati yanzu ba ta taso ba. Saboda haka ina shawartar Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi su kafa kwamiti mai karfi da zai duba abin da ya kamata a yi, domin dawo da martabar noma a kasar nan. Saboda ta haka ne kadai za a samu mafita, domin rikon sakainar kashin da ake yi wa noma bai dace ba.

Me ya sa wasu bangarori a wannan kasa suke kallon Arewa ci-baya?

Dalili shi ne rashin samun shugabanni masu kishi sai kishin aljihunsu. Su Sardauna ba haka suka yi ba, ci gaban kasa da yankinsu ne a gabansu har suka bar duniya. Ta haka aka samu ababen more rayuwa da asibitoci da makarantu da sauransu, abubuwan da maimakon a inganta su, sai kara kashe su ake yi. Wasu daga abubuwan da su Sardauna suka samar wa Arewa su ne Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya da Kwalejin Kimiyya da Kere-Kere ta Kaduna da Gidan Rediyon Tarayya na Kaduna da Masakar Arewa da Kamfanin Buga Jaridun New Nigerian da Gaskiya Ta Fi Kwabo. Da za a iya koma wa noma irin da, duk matsalolin da ake fuskanta na rashin aikin yi za su kau. Saboda haka duk kasar da ta rungumi sana’ar noma ba za ta tozarta ba, matasa ba za su shiga aikata miyagun halaye ba. Saboda ko daukar amfanin gona daga gona zuwa gida bisa rakumi ko jaki matashi yake yi zai samu na biyan bukatunsa, balle akwai ayyuka da dama a fannin noma.