Ya kamata a nada mutumin kirki ministan ilimi – Limamin Kalaba
Babban limamin masallacin Izala na Kalaba a Jihar Kurosriba, Shaikh Bashir Salihu Abuga ya shawarci Shugaban kasa Muhammadu Buhari da idan ya tashi nada ministoci ya nada ministan ilmi Musulmi, wanda ya karanci sunnah domin gyara abin da aka bata na tarbiyyar dalibai da ke makarantun kasar nan.Ya ce: “Duk wata alama da ake sanya […]
Babban limamin masallacin Izala na Kalaba a Jihar Kurosriba, Shaikh Bashir Salihu Abuga ya shawarci Shugaban kasa Muhammadu Buhari da idan ya tashi nada ministoci ya nada ministan ilmi Musulmi, wanda ya karanci sunnah domin gyara abin da aka bata na tarbiyyar dalibai da ke makarantun kasar nan.
Ya ce: “Duk wata alama da ake sanya wa Musulmi amfani da su a makarantu ko kuma hijabi da riga da wando da hula da a da can ake amfani da su ga dalibai sun cire wannan gaba daya sai a sanya mata masu konannen kai ko a sanya su koyi da dabi’un Turawa. Wannan abin takaici ne.”
Ya kara da cewa: “Gaskiya yana da kyau a samu mai ruhin addini da zai rike aikin nan da amana, wanda ba zai cutar da kasarsa ba da kuma al’umma. A nada wanda zai sanya a samu ingantaccen ilmi ba da wuru-wuru ba.”
Sannan ya jaddada bukatar da ke akwai na samun wata kafa kwakkwara da za a rika magana daya da ita kasar nan, musamman yadda za a rika tuntubar Shugaban kasa.
Wata hanya da malamin ya hango da za ta kara sanya zaman lafiya tsakanin al’umma ita ce, a rika ziyartar juna da jawo juna jika. Ya ce ta nan ne za a rika haduwa ana tattauna matsalolin da ke tsakanin juma kuma a nemo hanyoyin magance su.