Ya kamata a rika kashe barayin gwamnati – Shugaban APC
Shugaban riko na Jam’iyyar APC a Shiyyar Bauchi ta Kudu Alhaji Abdulkadir Lawan Gyangyan ya nuna damuwarsa bisa yadda jami’an tsohuwar gwamnatin kasar nan tun daga matakin jiha zuwa tarayya suka yi ta wasoso da kudin jama’a, sannan sun gagara kare rayuwa da dukiyoyin al’umma, inda a sakamakon haka mutane da dama suka rasa rayuwansu […]
Shugaban riko na Jam’iyyar APC a Shiyyar Bauchi ta Kudu Alhaji Abdulkadir Lawan Gyangyan ya nuna damuwarsa bisa yadda jami’an tsohuwar gwamnatin kasar nan tun daga matakin jiha zuwa tarayya suka yi ta wasoso da kudin jama’a, sannan sun gagara kare rayuwa da dukiyoyin al’umma, inda a sakamakon haka mutane da dama suka rasa rayuwansu a jihohin Arewa maso Gabas.
Alhaji Abdulkadir ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da Aminiya a ofishinsa da ke Bauchi a ranar juma’ar da ta gabata, inda ya ce: “Ina so mutane su fahimci cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi ragamar gwamnati ne a hannun dan koyo ya kuma samu lalitar gwamnatin kasar an sace biliyoyin Naira. Kuma tun lokacin da ya kama aiki yana kokarin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali ne a kasar nan. Yanzu an samu natsuwa a masallatai da coci-coci, babbar matsalar da ta addabi ’yan Najeriya ita ce tsadar abinci da matsalar man fetur kuma idan aka ci gaba da addu’a ga Shugaban kasa, tabbas cikin kankanen lokaci wadannan matsala za su zamo tarihi,” inji shi.
Alhaji Abdulkadir Gyangyan ya ce a duk lokacin da za a yi gyara dole sai an ji a jiki, ya ce duk wanda aka ga yana sukar Shugaban kasa ya jahilci abubuwan da aka aikata ne a zamanin tsohuwar gwamnati na sace kudin al’umma.
Shugaban ya ce ya kamata Najeriya ta fara aiwatar da hukuncin kisa a kan duk wanda aka samu ya saci kudin jama’a a lokacin da yake rike da mukamin gwamnati. Ya ce da za a fara kashe mutanen da suka saci kudin gwamnati, to da Najeriya ta zauna lafiya babu barayi. “kasashe irin su China idan suka kama mutum ya saci kudin gwamnati nan take suke aika mutum Lahira sakamakon haka an samu raguwar masu satar dukiyar gwamnati,” inji shi.
Ya ce gwamnatinsu ta APC ba ta zo Jihar Bauchi ba ne domin raba wa jama’a kudi, inda ya ce Gwamna Mohammed Abubakar ya karbi ragamar gwamnati kusan an lalata komai a jihar.
“Gwamnatinmu za ta ba da fifiko ne wajen shimfida ayyukan alheri tare da cika manyan alkawuran da aka dauka a lokacin kamfe, duk wanda yake tunanin za a rika daukar dukiyar jama’a ana rabawa ga wasu mutane ’yan tsiraru, to ya kamata ya sauya tunaninsa,” inji Gyangyan.