Ya kamata a rika tantance lafiyar ’yan siyasa kafin yin takarar mukami?

Shugabanci babban al’amari ne wanda ke bukatar mutum mai cikakkar lafiyar jiki da ta kwakwalwa. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a rika tantance lafiyar ’yan takarar shugabanci a Najeriya tun kafin su shiga takarar neman wani mukami? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa: Ya dace […]

Ya kamata a rika tantance lafiyar ’yan siyasa kafin yin takarar mukami?
Ya kamata a rika tantance lafiyar ’yan siyasa kafin yin takarar mukami?

Shugabanci babban al’amari ne wanda ke bukatar mutum mai cikakkar lafiyar jiki da ta kwakwalwa. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a rika tantance lafiyar ’yan takarar shugabanci a Najeriya tun kafin su shiga takarar neman wani mukami? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:

Ya dace a rika tantance lafiyarsu – Usman Ibrahim

A.A. Masagala, a Benin

Ni a ra’ayina, babu shakka ya dace a yi aiki da wannan tsarin na tantance hankalin dan takara kafin ma ya ce ya tsaya takarar kowane mukami a cikin jam’iyyar da yake bi, domin yin hakan zai tabbatar da wanda ya dace ya shugabanci jama’a kuma idan aka yi aiki da wannan tsarin zai tsaftace mana dimokuradiyya a Najiriya kwarai da gaske; domin duk mai hankali ya san shugabanci yana bukatar nagartaccen mutum mai hankali, mai ilimi, mai gaskiya, mai adalci, mai hakuri da tausayi, wanda ba zai nuna bambanci ba a cikin shugabancisa. Saboda haka abu ne mai kyau a auna kwakwalwar mutum kafin ya zama shugaban jama’a. Wannan daidai ne, babu sabani a ciki. Na goyi bayan wannan dari bisa dari.”

Lallai a rika bincikar lafiyar ’yan takara – Ahmadu Koromi

A.A.M.asagala, a Benin

Ahmadu Koromi Mai Turare: “Ni a ganina, abin da dimokuradiyyar kasar nan ta dade take bukata ke nan saboda haka a gaskiya ya dace kuma na goyi bayan wannan shirin. Idan an tabbatar da shi lallai na san kowa sai ya ji dadi. Dalilina shi ne, idan aka samu shugabannin da aka tantance hankulansu daga kwararrun likitoci na kwakwalwa, to lallai babu shakka za a sama maslaha cikin shugabanci na jama’a kuma ba sai na siyasa kadai ba, ko da sarkin tasha ne; a tantance hankalinsa kafin a ba shi ya zama sarkin tasha.

Bai kamata a tantance lafiyar ’yan takara ba – Ibrahim Abdul’aziz

Rabilu Abubakar, a Gombe

Ibrahim Abdul’aziz: “A ganina, babu ruwan siyasa da lafiyar dan takara. Muddin idan mutum yana da manufa mai kyau bai kamata a tsaya ana batun mai lafiya ne ko marar lafiya ba. Siyasa ba a hada ta da rashin lafiya, ko mutum bai da lafiya muddin ya cancanta a bar shi kawai ya yi siyasarsa, domin rashin lafiya ba ya kawo mutuwa. Mu duba misalin Jihar Kaduna, inda Ahmad Makarfi ya yi mulkin tsawon shekara takwas, ya sauka kuma ya zama Sanata bai mutu ba kamar yadda a lokacin da yake mulki aka dinga cewa ba zai iya ba, ba shi da lafiya. Sai ga shi masu lafiya da yawa sun mutu sun bar shi bai mutu ba. Don haka siyasa ba ruwanta da cuta ko ciwo, cancanta kawai ake nema.”

Ya dace a tantance lafiyar ’yan siyasa – Harirah Abdulssalam

Rabilu Abubakar, a Gombe

Harirah Abdulssalam: “Ni ina mai ra’ayin ganin ya dace a fara tantance lafiyar ’yan siyasa kafin su shiga takarar mukami kowane iri ne, domin lafiya ita ce komai. Idan ba lafiya ba yadda za a yi a samu yadda ake so. Kamar yadda tsohon Shugaban kasa, marigayi Umar Musa ’Yar’aduwa ya hau karagar mulkin kasar nan bai da koshin lafiya, wanda hakan ya sa daga karshe mulki ya kubuce wa Arewa ya tafi Kudu ba tare da wa’adin ’yan Arewan ya kare ba. Ai ko Bahaushe ma ya yi magana, inda ya ce lafiya uwar jiki idan ba lafiya ba yadda za a yi mutum idan ya ci zabe ya iya gudanar da komai ya tafi daidai. Don haka ni ina mai ra’ayin a fara tantance lafiyar ’yan siyasa, yin haka abu ne mai kyau.”

Ya kamata a rika duba lafiyarsu – Barista Muhammad

Muhammad Yaba, a Kaduna

Barista Muhammad Bello Umar: “Ya kamata a rika duba lafiyarsu, musamman idan aka yi la’akari da yadda suke sata da almundahana da dukiyar kasa. Amma akwai bukatar a yi gyra a kundin tsarin dokar kasa saboda idan ba a saka a doka cewa duk wanda zai tsaya takara dole sai an duba lafiyarsa ba, mafi akasarinsu za su rika zuwa kotu domin ganin ba a hana su takara ba. Amma dai ya da ce a rika duba lafiyarsu.”

Ya dace a tantance lafiyarsu – Zubairu Sham’una

Muhammad Yaba, a Kaduna

Alhaji Zubairu Sham’una: “kwari, ina goyan bayan a rika duba lafiyar duk wani dan takara, ba ma lafiyar jikinsa ba kawai hatta ta kwakwalwarsa saboda wasu abubuwa da wasu shugabannin ke yi yana sanyawa ka rika tambayar kanka ko mutum da lafiyarsa yake aikata abin da yake aikatawa kuwa? Misali, akwai shugaban karamar Hukuma a Kaduna, wanda har ya kammala wa’adinsa bai da cikakkiyar lafiya. Wannan ya sa nake goyon bayan a rika duba ko gwada lafiyar duk ’yan takara kafin su shiga zabe.”