Ya kamata a rushe kungiyar Gwamnonin Najeriya – Sarkin Arewan Bauchi
Alhaji Hassan Muhammad Sharif, shi ne Sarkin Arewan Bauchi kuma Shugaban kungiyar Samar Da Zaman Lafiya da kuma Kyakkyawan Shugabanci a Arewa. A ganawarsa da Aminiya, ya tabo batun siyasar kasar nan kamar haka: A kwanakin baya Shugaban Ma’aikatan Najeriya ya gargadi ma’aikatan gwamnati su guji karbar sarautun gargajiya, kasancewarka daya daga cikin masu sarauta, […]
Alhaji Hassan Muhammad Sharif, shi ne Sarkin Arewan Bauchi kuma Shugaban kungiyar Samar Da Zaman Lafiya da kuma Kyakkyawan Shugabanci a Arewa. A ganawarsa da Aminiya, ya tabo batun siyasar kasar nan kamar haka:
A kwanakin baya Shugaban Ma’aikatan Najeriya ya gargadi ma’aikatan gwamnati su guji karbar sarautun gargajiya, kasancewarka daya daga cikin masu sarauta, shin ka goyi bayan hakan ko kuma?
Wannan magana ce murdaddiya, kuma ba ta da ma’ana sosai, domin sarauta iri-ire ce. Kamar irin karramawar da gwamnatin tarayya take yi ne, idan ka yi fice a wani bangare sai ka ga ta ba ka lambar yabo. Idan sarauta ce haka wannan babu laifi, idan kuma sarauta da ta hada da dagatai da hakimai da sauran masu kasa ne, wannan kam bai dace ba. Yin hakan zai sanya a rika karbar albashi biyu, kuma zai raba wa wanda ya karba hankali.
Akwai batun rikici tsakanin Fulani da manoma, kasancewar kana daga cikin masu sarauta, baya ga haka kai ne shugaban kungiyar samar da zaman lafiya a Arewa, ko akwai wani yunkuri da ka yi ko kungiyarku ta yi a kan wannan batun?
Wannan rikici abu ne da muka gada, Fulani da manoma sun dade suna zumunci, sun kuma dade suna batawa. Mun yi bakin kokarinmu wurin fadakar da su muhimmanci zaman lafiya, domin idan babu zaman lafiya ba za a yi noma da kuma kiwon ba, don haka ina kira gare su su tsare mutuncin juna.
A yanzu babu batun da yake ci wa Arewa tuwo-a-kwarya kamar sha’anin tsaro, ko kana da wani abu da za ka ce a kai?
Tabbas al’amarin ya fi shafar Arewa, kuma abin bakin ciki ne. Kamata ya yi manyanmu da yaranmu a tashi tsaye a ci gaba da addu’o’i, domin addu’a ba ta yawa, ina da yakinin idan an yi hakan za a shawo kan matsalar ta zama tarihi da izinin Allah, wadanda suke da hannu ko suke aikata hakan Allah Ya shirye su, idan ba ma su shiryuwa ba ne kuma Allah Ya karya su.
Babu abin da yake tashe a siyasar Najeriya kamar rikicin da ya kunno kai cikin kungiyar Gwamnonin Najeriya tun bayan da suka yi zabe, wanda har yau ba a kai ga cim ma maslaha ba, ko a kwanan nan ma an jefi wadansu gwamnonin arewa a Jihar Ribas, ko me za ka ce kan hakan?
Ni ban yarda da kungiyar ba ma, domin ba ta da wata ma’ana, suna yinta ne kawai don su danne talakawa. Abin kunya sun kasa hada kansu, wanda kuma da su ya kamata a yi koyi. Na san kundin tsarin mulkui bai hana su ba, amma abin da nake so a duba shi ne, shugaban kasa na nan, ’yan majalisun tarayya na nan, haka akwai gwamna da ’yan majalisun dokoki na jihohi, sannan kuma a ce ga wata kungiya ta gwamnoni, idan haka ne mene ne amfani majalisun?
Kowace jiha tana da matsaloli da ayyukan da ta sa a gaba, to me ya sa za su hadu su ce sai abin da suka tsara? Muna rokon Allah Ya wargaza ta saboda ba ta da wani amfani. Na ji wani gwamna yana ce wai arewa ce ta ware ta zabe wani, wannan rashin kwarewa a siyasa ne. A takaice dai ya kamata a sanya a kundin tsarin mulki a rushe kungiyoyin gwamnoni da na shugabannin kananan hukumomi, saboda ba su da amfani. Abin da ya kamata shi ne shugaban kasa ya kira ’yan majalisarsa su tattauna abin da za su tattauna, gwamna ma ya tattauna da ’yan majalisarsa shi ke nan a gudanar wa mutane ayyukan ci gaba. Wadannan kungiyoyin ne suka lalata kasa, domin zan iya tuna lokacin Shagari shugaban kasa na nan, shugabannin jam’iyya ma na nan, ko a lokacin Tatari ke Gwamnan Jihar Bauchi da kansa yake zuwa gidan shugaban jam’iyya Kari Bajoga, idan kuma ya yi abin da bai dace ba za su kira shi har ofishin jam’iyya su kuma tuhume shi, amma a yanzu ba haka ba ne.
A yanzu ga sabuwar jam’iyyar APC ta shigo, kuma ana rububi a kanta, kana ganin za ta zama barazana ga jam’iyyarku ta PDP?
E, to, ya danganta, abin da yake damun siyasar Najeriya shi ne, ba a damu da manufofin jam’iyya ba, ba a kuma damu da kyawun ’yan takara ba. Ba ma wannan ba abin da nake so talakawa su bincika shi ne, wadannan jam’iyyu da suka hade shin ba sa mulki a wadansu jihohi ne? Idan suna yi, shin me suka yi wa talakawa fiye da na jam’iyyar PDP? Idan sun fi PDP shi ken an, idan kuma ba su fi ba to talakawa su fahimci inda jam’iyyar ta dosa. Abin da nake mutane su fahimta shi ne, a yanzu idanun jama’a sun rufe burinsu kawai a taru a kayar da PDP ba wani abu ba. A yanzu za a samu dan PDP mutumin kirki, amma da yake a PDP yake sai ka ga wani mutumin banza ya kayar da shi. Wannan ba daidai ba ne. Da yawa daga cikin ’yan APC suna da alaka da PDP, rashin samun nasara ya suka bar PDP ne, don haka babu wani abu da APC za ta iya yi wa PDP.