Ya kamata a tausaya min saboda halin da na shiga —Rahama Sadau
Ta dauki abin da ya faru sakamakon hotunan da ta wallafa a matsayin kaddara.
Rahama Sadau ta bayyana cewa ta yi nadamar abubuwan da suka faru a sanadin hotunan da ta wallafa.
Jarumar ta bayyana hakan ne a yayin hirarta da sashen Hausa na BBC, inda ta ce ya kamata jama’a su tausaya mata saboda halin da ta shiga.
- ‘Yan Kannywood sun yi tir da hotunan Rahama Sadau
- Rahama Sadau ta yi nadamar batancin da hotunanta suka jawo
- Kungiyar shirya fina-finai ta dakatar da Rahama Sadau
- Lokuta hudu da Rahama Sadau ta jawo cece-kuce a Kannywood
“Na bayyana a cikin bidiyon dana yi, na yi nadamar abin da ya faru.
“Ya kamata mutane su fahimce ni, a matsayina na cikakkiyar Musulma ba zan taba yin abin da zai jawo batanci ga Manzon Allah S.A.W ba,” cewar Rahama.
Ta bayyana cewa ta wallafa hotunan ne da daddare kamar yadda ta saba kuma ta kwanta barci.
Washegari da safe ta tashi ta iske sakkoni sama da 10,000 wanda daga bisani aka jawo hankalinta game da abin da ke faruwa.
Jarumar ta ce kamata ya yi a ce jaruman fim takwarorinta a masana’antar Kannywood su ja hankalinta tun farko.
Rahama Sadau ta kara da cewa ta dauki abin da ya faru a matsayin kaddara, saboda kowane dan Adam da irin yadda kaddararsa ke zuwa.
Hotunan da jarumar ta wallafa, wanda suka kai ga wani ya yi batanci ga Manzon Allah SAW, ya jawo sa dimbin mutane, har da jaruman Kannywood tofa albarkacin bakinsu.
Wasu na mata nasiha da jan hankali, wasu kuma na caccakar ta saboda yadda abin da ta yi ya jawo aka taba darajar Fiyayyen Halitta, Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam.