Ya kamata a tura karin dakaru iyakokin Najeriya — Majalisar Wakilai
Dukkanin shirin afuwar da aka yi a kasar sun gaza cimma muradun da aka samar da su a karkashi.
Majalisar Wakilai ta bukaci rundunar sojoji ta tura karin dakaru don samar da tsaro a iyakar Jihar Sakkwato.
Majalisar ta yi wannan kiran ne domin kawo karshen amsar kudin da masu ikirarin jihadin kasashen Jamhuriyar Nijar da Mali da kuma Libya ke yi a hannun mazauna yankunan da ke kan iyakokin kasar.
- Matakan Tinubu 12 na wadata ƙasa da abinci
- NAJERIYA A YAU: Illar cin bashi daga kamfanonin bayar da bashi ta waya
Dan majalisar da ke wakiltar mazabar Tangaza da Gudu na Jihar Sakkwato, Sani Yakubu ne ya gabatar da kudiri a zauren majalisar.
Honarabul Yakubu ya bayyana cewa ’yan ta’adda na amfani da dazukan Tsauna da kuma Kuyan Bana da dukkaninsu suka ratsa har cikin Jamhuriyyar Nijar, wajen aikata ta’addancinsu.
A cewarsa, kungiyoyin ’yan ta’addan da ke yankin da a baya basa ga maciji da juna a yanzu sun hade waje guda, inda suka sha alwashin hana ayyukan noma da kiwo, wanda ke matsayin sana’ar mutanen yankin, lamarin da kuma ke kara jefa rayuwar mutanen yankin cikin garari.
Dan majalisar ya ce idan har ba a dauki matakan da suka kamata ba, hakan zai kara haddasa matsalar karanci abinci a sassan Najeriya, lura da gudunmawar da yankin ke bayarwa wajen samar da abinci a kasar.
Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da shugaban rundunar sojojin kasa na kasar, Manjo Janar Taoreed Lagbaja ya shaida wa Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal cewar dukkanin shirin afuwar da aka yi a kasar sun gaza cimma muradun da aka samar da su a karkashi, maimakon haka ma sake baiwa ‘yan ta’adda damar dunkulewa waje guda ya yi don kaiwa al’umma hari.