Ya kamata a yi wa aikin majalisa garambawul
Tuni aka fara kiraye-kirayen cewa dole idan sabon Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari na so ya yi nasara a mulkinsa, to sai ya fara yakar cin hanci da rashawa a Majalisar Dokoki ta Tarayya. Tsohon Ministan Birnin Tarayya, kuma zababben Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i ya taba fallasa yadda wasu manyan ’yan Majalisar Dattawa […]
Tuni aka fara kiraye-kirayen cewa dole idan sabon Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari na so ya yi nasara a mulkinsa, to sai ya fara yakar cin hanci da rashawa a Majalisar Dokoki ta Tarayya. Tsohon Ministan Birnin Tarayya, kuma zababben Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i ya taba fallasa yadda wasu manyan ’yan Majalisar Dattawa suka bukaci ya ba su toshiyar baki ta Naira miliyan 50 kafin su tantance shi a matsayin Minista.Wannan ya jawo ka-ce-na-ce; kuma ya kara haskaka yadda rubabbun mutane suka cika majalisar. Mun ga yadda tsohon dan Majalisar Tarayya, Faruk Lawan ya wulakanta, bayan an nadi maganarsa a bidiyo, inda fitaccen dan kasuwar nan Femi Otedola ke masa alkawarin ba shi cin hanci domin ya wanke kamfaninsa na Forte oil daga badakalar tallafin mai.
Kazalika, Dokta Haruna Yarima, wani tsohon jajirtaccen dan majalisa ya taba tona asirin yadda manyan kamfanonin sadarwa ke bai wa ’yan majalisa cin hanci ta hanyar ba su katin waya kyauta, don su ci gaba da yin yadda suka ga dama.
Hakika da walakin goro a miya, cewa tunda muka dawo dimokuradiyya, babu abin da ’yan siyasa suka yi fice a kai, kamar badda sawun kudin jama’a, amma abin mamaki muna da majalisa wadda cikin aikinta har da sanya ido a kan ma’aikatu da hukumomin gwamnati don ganin almundahana da sace kudin al’umma ba su samu gindin zama ba, amma a banza kamar an shuka dusa. Babu abin da ya sauya, maimakon raguwa ma, satar sai ta ci gaba da habaka daga neman cin hancin Naira miliyan 50 ta koma sace tiriliyoyin Naira.
Yau ga majalisar da ta dakile Maina da ya fara bankado ta’asar sama da fadi da kudin ’yan fansho. Maimakon kwamitin su Kabiru Gaya ya maida hankali wajen ganin an kwato wa ’yan fansho hakkokinsu, sai suka koma farautar Maina.
’Yan Najeriya ba su yi dace da ’yan majalisa masu kishin kasa ba; sai ’yan cuwa-cuwa ko ’yan damfara da siyasa, wadanda suna majalisar ce, domin su hada baki a zambaci kasa.
Tsohon dan Majalisar Tarayya kuma Gwamnan Jihar Binuwai mai barin gado, Gabriel Suswam ya taba cewa cikin ’yan majalisar 360 duka-duka masu amfani ba su wuce mutum 20 ba. Ya ce sauran duk cima-zaune ne, wasu ko karatu da maganar kirki ba su iyawa, haka nan ake kwasar dukiyar al’umma ana biyansu.
Kazalika tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi Na II, ya taba fadin yadda ’yan majalisar marasa amfani ke lakume kashi 25 cikin 100 na kasafin kudin Najeriya a shekara.Wannan ya sake bude wani sabon babi na muhawara, inda ’yan Najeriya suka fara nazarin majalisar da ayyukanta da kuma nasarorinta. Daga karshe dai gaskiya ta yi halinta, domin kowa ya fahimci cewa mutanen da ke majalisar, mutane ne masu son zuciya da son rai kawai. Kullum me za su samu shi ne ke gabansu. Aikin majalisa, bai kai noma wahala ba, amma kudin da ake ba su, masu aikin gaskiya na ci gaban kasa ba su samun daya bisa gomansa. Su tatsi ma’aikatun gwamnati lokacin duba kasafin kudi, su amshi na goro daga kamfanoni masu zaman kansu kamar su GLO da MTN da kamfanonin mai da sauransu, kuma a hada baki da su a zambaci kasa.
Saboda makudan kudin da suke samu ya sa, a lokacin zabubbukan fidda-gwani, suka maida abin a mutu ko a yi rai.
Misali a Katsina, wasunsu babura suka rika raba wa deleget domin su sake komawa su ci gaba da sharbar romo.
Yanzu kiraye-kirayen da kowa ke yi, shi ne yaya za a yi a rage cin amanar kasa da ’yan majalisar ke yi? Yaya za a yi su taimaka wa sabuwar gwamnati ta gina kasa? Gaskiya barawo ba zai iya hana sata ba, akwai babban kalubale ga Baba Buhari wajen yakar kurayen da ke majalisun. Mutane ne da babu ruwansu da kowa sai lokacin zabe.
Hakika na yi imanin mafi yawancin ’yan majalisar kasar nan ba su da kishin kasa.Wannan ya sa muke ganin kamata ya yi a yi wa baki dayan aikin majalisa garambawul, a maida shi aiki marar armashi, ya zama sai ’yan kishin kasa ne kawai ba ’yan kasuwa ba za su yi sha’awar aikin. Ba masu zuwa suna kwana a manyan otel-otel a Abuja, suna surutan wofi da rigimar neman iko, suna barin mutanensu cikin ragga ba.
Kwamared Bishir Dauda Sabuwar Unguwa Katsina
Babban Sakataren kungiyar Muryar Talaka ta kasa
08165270879