Ya kamata Bafarawa da Wamakko su sasanta – Sakkwatawan Abuja

Al’ummar Sakkwatawa mazauna Abuja sun yi kira ga Gwamnan Jihar Sakkwato, Aliyu Wamakko da tsohon Gwamnan Jihar Attahiru Bafarawa su sasanta tsakaninsu game da rikicin shugabanci da ke gudana a Jam’iyyar APC reshen jihar. Alhaji Muhammad Abubakar Sakkwato, wanda aka fi sani da Abu Abuja ne ya yi wannan kiran a madadin ’ya’yan kungiyar Sakkwata […]

Ya kamata Bafarawa da Wamakko su sasanta – Sakkwatawan Abuja
Ya kamata Bafarawa da Wamakko su sasanta – Sakkwatawan Abuja

Al’ummar Sakkwatawa mazauna Abuja sun yi kira ga Gwamnan Jihar Sakkwato, Aliyu Wamakko da tsohon Gwamnan Jihar Attahiru Bafarawa su sasanta tsakaninsu game da rikicin shugabanci da ke gudana a Jam’iyyar APC reshen jihar. Alhaji Muhammad Abubakar Sakkwato, wanda aka fi sani da Abu Abuja ne ya yi wannan kiran a madadin ’ya’yan kungiyar Sakkwata mazauna Abuja a yayin da yake zantawa da manema labarai,a Abuja inda ya ce, Sakkwatawa mazauna Abuja suna matukar damuwa da abin da ke faruwa a jihar tunda Gwamna Wamakko ya koma APC. Abu Abuja ya ce rikicin da APC ke fuskanta a Jihar Sakkwato matsala ce ta siyasa da za ta iya wucewa idan har aka tattauna tsakanin juna. “A siyasa, dole ne a samu sabani tsakanin al’umma amma da yardar Allah, manyan ’yan siyasar biyu za su sasanta nan ba da jimawa ba,” inji shi. “Ya kamata Bafarawa da Wamakko su zauna tare, su tattauna abin da zai amfani al’ummar jihar. Na yi amanna cewa za su fahimci juna kuma su hada hannu domin bunkasa jam’iyyar. Su din ne dai za su raini jam’iyyar, domin dukkansu ’ya’yan tsohuwar Jam’iyyar ANPP ne a baya,” inji Abu Abuja. Ya ce, Wamakko bai shiga Jam’iyyar APC domin neman mukami ba, sai domin yadda ya tuntubi al’ummar Sakkwato kuma suka ba shi goyon baya, kamar dai yadda abin ya kasance a can baya, lokacin da ya bar ANPP zuwa PDP.