Ya kamata Buhari ya kafa hukumar karbe makamai daga hannun jama’a – Adaji

Mista Ben Adaji na daya daga cikin manyan ’ya’yan Jam’iyyar APC a Jihar Kogi a hirarsu da wakilinmu a Jalingo, Mista Adaji ya sharwarci Shugaban kasa mai jiran gado Janar Muhammadu Buhari ya kafa wata hukuma ta musamman da za ta karbe makamai daga hannun jama’a don tabbatar da zaman lafiya a cikin kasa: Aminiya: […]

Ya kamata Buhari ya kafa hukumar karbe makamai daga hannun jama’a – Adaji
Ya kamata Buhari ya kafa hukumar karbe makamai daga hannun jama’a – Adaji

Mista Ben Adaji na daya daga cikin manyan ’ya’yan Jam’iyyar APC a Jihar Kogi a hirarsu da wakilinmu a Jalingo, Mista Adaji ya sharwarci Shugaban kasa mai jiran gado Janar Muhammadu Buhari ya kafa wata hukuma ta musamman da za ta karbe makamai daga hannun jama’a don tabbatar da zaman lafiya a cikin kasa:

Aminiya: Akwai matasalar makamai a hannun jama’a, a ganinka me ya kamata zababben Shugaban kasa zai yi don magance wannan matsala?
Ben Adaji: Nasarar da Janar Muhammadu Buhari ya samu dama ita ce abin da ’yan Najeriya suke bukata. Saboda haka abin da ya kamata Janar ya yi in ya karbi ragamar mulki shi ne duk abin gwamnatin PDP a karkashin Jonathan ta bata, to a gyara. Janar Buhari ya tabbatar cewa kowa na bin doka domin kasa ba ta ci gaba in ba a bin doka. Kuma akwai bukatar ya maida hankalinsa wajen hada kan ’yan Najeriya ta hanyar tafiyar da shugabanci mai kyau kada ya nuna bambanci a tsakanin al’ummar kasa, wannan zai taimaka wajen kawo zaman lafiya da bin doka kuma ta haka za a samu ci gaba mai inganci a kasar nan.
Na biyu akwai bukatar Shugaba Buhari da zarar ya hau kujerar mulki ya kafa wata hukuma da za ta karbe makamai daga hannun jama’a, domin akwai manyan bindigogi da kanana a hannun jama’a wadanda da su ne ake amfani wajen aikata miyagun laifuffuka da yake-yake a wasu sassan kasar nan. Gwamnatin Jonathan ta kasa daukar wani mataki wajen shawo kan yawan aukuwar yake-yaken da suke faruwa a cikin kasa, saboda ta gaza wajen hukunta masu hannu a cikin wadannan fadace-fadace da suka yi sanadiyyar asarar rayuka masu yawan a sassan da kasar nan.
Don haka Janar Buhari ya kafa kwamiti karbar makamai daga hannun jama’a, kuma da zarar an kafa wannan kwamiti sai a yi shela a bayar da wa’adin makonni ko wata cewa kowa ya maida wa hukuma makamin da ke hannunsa kuma a tanadi hukunci mai tsanani ga duk wanda aka samu da makami bayan wa’adin da aka bayar ya wuce.
Aminiya: A ganinka wadanne sassa na kasar nan ne wannan lamari na makamai a hannun jama’a ya fi muni kuma ta yaya kake ganin za a samu nasarar karbe makamai daga hannun jama’a?
Ben Adaji: Wannan batu na a karbe makami daga hannun jama’a da ake kira da Turanci (dis-armament) na da muhimmamci wajen tabbatar da zaman lafiya a kasa, ga misali kowa ya san cewa akwai makamai masu yawan gaske a hannun jama’a a jihohin Ribas da Bayelsa sai kuma yankin jihohin Arewa maso Gabas wadanda suka hada da jihohin Borno da Yobe da Adamawa da Bauchi da kuma Taraba. Kuma ba wai a wuraren da na lissafa kawai ne ke da wannan matsala ba, kusan sai in ce kowane bangare na kasar nan akwai wannan matsala sai dai wani bangaren lamarin ya fi wani muni. Kowa ya san san irin sakacin da gwamnati mai barin gado ta yi ta fuskar tsaro wanda lamarin ya kai inda muke a halin yanzu. A wannan yankin kowa ya san san an samu matasalar Boko Haram sa’an nan kuma Jihar Taraba akwai matsalar yake-yaken kabilanci da addini wadanda suka sa akwai makamai a hannun jama’a kuma ya zama tilas gwamnati ta karbe wadannan makamai don dorewar zaman lafiya.
Aminiya: Kana ganin ta wace hanya ce makaman suka shiga hannun jama’a duk da kasancewar akwai jami’an tsaro a kan hanyoyi da tashoshin jiragen ruwa da na sama a kasar nan?
Ben Adaji: To, in akwai gwamnatin da ba ta da gaskiya kuma ba ta damu da kare rayukan jama’a ba, to komai zai iya faruwa. Kuma jami’an tsaron da ke kan hanyoyi suna da laifi domin yawancin suna sane da yadda ake wucewa da wadannan makamai, amma saboda rashin kishin kasa ba su yi komai ba.
A kashin gaskya gwamnati ce mai laifi domin ita ce ake zargi da bai wa ’yan Boko Haram makamai. Kowa ya san cewa akwai makamai masu yawa da aka kama wadanda aka ce wai na gwamnati ne amma daga baya ba wanda ya san inda aka kai makaman. Ina kara nanata cewa akwai muhimmancin gaske shi Janar Buhari ya tabbatar cewa an aiwatar da shiri na musamman wajen karbe makamai daga hannun jama’a. Kuma a tafiyar da aikin kan gaskiya ta yadda ba za a bar wani wajen hukunci ba, komai matsayinsa kamar yadda muka gani a lokacin mulkin Jonathan. A yi gaskiya ko ta ina, wato kada a kama wani da makami a bar shi saannan a samu wani da makami a ce za a hukunta shi. Ya zama tilas duk wanda aka samu da laifi a hukunta shi ta haka ne za a samu zaman lafiya a kasar nan.

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu