Ya kamata Buhari ya karbo dukiyar da aka sata a Najeriya

Tun bayan da hukumar zabe mai zaman kanta ta bayyana Janar Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da ta gudanar a ranar 28 ga watan Maris,mutane suka fara kiraye-kirayen cewa ya dace Janar din ya bankado ta’asar da aka tafka musamman satar dukiyar gwamnati,da aka dauki shekara da […]

Ya kamata Buhari ya karbo dukiyar da aka sata a Najeriya
Ya kamata Buhari ya karbo dukiyar da aka sata a Najeriya

Tun bayan da hukumar zabe mai zaman kanta ta bayyana Janar Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da ta gudanar a ranar 28 ga watan Maris,mutane suka fara kiraye-kirayen cewa ya dace Janar din ya bankado ta’asar da aka tafka musamman satar dukiyar gwamnati,da aka dauki shekara da shekaru ana yi,wandan ake zargin shugabannin kasar da yi.To sai dai a jawabinsa bayan ya karbi takardar shedar lashe zabe daga hannun Attahiru Jega,shugaban hukumar INEC ta kasa,shugaban kasa mai jiran gado,Janar Muhammad Buhari,ya bayyana cewa “Zai ja layi”.Wannan jan layi da ya ce gwamnatinsa za ta ja,ya jawo fassara daban -daban.Wasu suna ganin kamar Shugaban yana nufin cewa duk wadanda suka saci dukiyar gwamnati ke nan sun ci bulus,ba za a tursasa masu su amayo ta ba.Wasu kuma suna ganin Janar din kawai yana kokarin sayen lokaci ne,inda da zaran an rantsar da shi,zai fara duka da sandarsa ga wadanda suka ci amanar kasa.

To ko ma me Janar din yake nufi da “Jan layi”, maganar gaskiya ya kamata a tuhumi barayin kudin gwamnati.Abin da ya sa Janar yake da kima da mutunci a idon duniya shi ne,gaskiyarsa da rikon amanarsa da kuma bin doka da oda.Don haka duk wani sassauci ta wannan bangaren zai nuna kawai Janar yana neman ci gaba daga inda suka tsaya,abin da Bature yake kira da maintaining the status kou.
Daga 1986 zuwa yau,Allah kadai ya san tiriliyan nawa shugabanin Nijeriya suka sace.Tun daga badakalar dalar Amurka biliyan 12 da ake zargin tsohon Shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida da batarwa,zuwa kwantena-kwantena ta kudin da ake yayata cewa Abdussalami Abubakar ya karkatar da su zuwa wani wuri.Har zuwa biliyoyin naira da aka sace a karkashin mulkin Shugaba Obasanjo da sunan sayar da kadarorin gwamnati da gyara wutar lantarki,kuma ba a gyara wutar ba.sannan an sace kudin.Sata ta rashin hankali da aka gani a karkashin wannan gwamnati , a ce duk an manta da wadannan ,to ba a yi wa ‘yan Najeriya adalci ba,kuma ba a nemi a gyara kasar nan ba.
Damke barayin gwamnati,da ‘yan kwangila wadanda ake hada baki a zambaci gwamnati tare, da tuhumar duk wanda ake zargin yana da hannu a wajen sace kudin talakawa ,zai taimaka wajen jan layi da kawo karshen sata da shugabanni masu rike da mukami suke tafkawa.Bincike da kwato kudin sata daga hannun shugabanni ba wani sabon abu ba ne a duniya.A Nijeriya,mun ga yadda Janar Murtala Ramat Muhammad ya gudanar da yaki da cin hanci da rashawa,inda ya kafa kwamiti,suka kuma gudanar da bincike suka fitar da farar takarda,wadda kafin a fara aiwatar da ita,aka kashe murtala ranar 12 ga watan Fabarairu,daga cikin abin da farar takardar ta kunsa har da kwace kadarorin barayin Shugabanni da haramta masu siyasa baki daya da garkame su a gidan yari.Duk da cewa wannan ya faru a karkashin mulkin soja inda kundin tsarin mulki irin na Dimokuradiyya bai yi aiki ba,sai dai dokoki irin na soja.To amma ya kamata a duba a ga shin kundin tsarin mulkinmu na yanzu ya amince a kafa irin wannan kwamiti na bincike da Janar Murtala ya taba kafawa? Sannan ya ya za a aiwatar da shawarwarin kwamitin. ‘Yan Nijeriya za su amince cewa aiwatar da haka ne kawai zai sa mutane masu niyyar ci gaba da azurta kansu da kudaden haramun za su sha jinin jikinsu.’Yan Nijeriya za su so Buhari ya binciki kudaden da Abdussalamu Abubakar da Obasanjo suka karbo daga iyalan Janar Sani Abacha.Ina kudaden suke? Me aka yi da kudaden? Nawa ne suka karbo? Duk ‘yan Nijeriya za su so sanin haka.Amma kuskure ne,Janar Buhari ya yi shiru ya kame bakinsa a kan wannan zalincin da aka aikata musamman daga 1986 zuwa yau.Duk wani yunkuri na jan layi zai nuna ke nan akwai wasu mutane da ake shakkun tabawa a Nijeriya.Ina kudaden bayin Allah ‘yan fansho? Ina kudaden takin zamani? Ina kudaden tallafin mai da na kalanzir? Ina kudaden da aka samu a wajen sayar da kadarorin Nijeriya wanda hukumar BPE ta yi daga 1999 zuwa yau? Ina barayin ‘yan kwangila wadanda ke karbar kudi ba tare da sun yi aikin ba? Ina kudaden da ake sacewa a hukumar NNPC? Duk ‘yan Nijeriya suna kishirwar ganin Janar Muhammadu Buhari ya dauki kwakkwaran mataki a kansu.

Kwamared Bishir Dauda
Sabuwar Unguwa Katsina
Babban Sakataren kungiyar
Muryar Talaka ta kasa
08165270879