Ya kamata Buhari ya kwato kudin gidauniyar Boko Haram -Dokta Muri
Bayan shekara daya da tsohuwar gwamnatin Jonathan ta kafa gidauniyar tallafa wa wadanda Boko Haram suka tagayyara wadda aka kaddamar a ranar 17 ga Yunin 2014, har yanzu jama’a ba su san inda gidauniyar ta fuskanta ba. Aminiya ta tuntubi wani masanin tarihi kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum Dokta Aliyu M. Muri […]
Bayan shekara daya da tsohuwar gwamnatin Jonathan ta kafa gidauniyar tallafa wa wadanda Boko Haram suka tagayyara wadda aka kaddamar a ranar 17 ga Yunin 2014, har yanzu jama’a ba su san inda gidauniyar ta fuskanta ba. Aminiya ta tuntubi wani masanin tarihi kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum Dokta Aliyu M. Muri na Sashin Tarihi na Jami’ar Umaru Musa da ke Katsina, kuma shugaban kungiyar masu gwagwarmayar farfado da martabar Arewa don jin ta bakinsa kan lamarin:
Aminiya: Me ake ciki game da gidauniyar da tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kafa don tallafa wa wadanda rikicin Boko Haram ya shafa?
Dokta Muri: Wato akwai tambayoyi da yawa a kan ita waccan gidauniya. Na farko babu wanda zai iya gaya maka nawa aka tara? Tun lokacin da aka yi wannan taro nawa ya karu da sauransu. Sannan kudin nan ina suke? Wadanda suka yi alkawurra sun cika? Kudin nan suna ina a halin yanzu,wane banki suke? Wadanda suka yi alkawurra ba su cika ba yaya za a yi da su? Akwai kwamitin karbar mulki da aka yi, shin wadannan kudi an sanya su cikin wadanda za a mika ga sabuwar gwamnatin? Wadannan wasu ne daga cikin tambayoyin da ya kamata a amsa.
Abu muhimmi shi ne a san cewa, bara ba ta iya tasirin da za ta kawo waraka ga barnar da aka aiwatar game da Boko Haram. Don wannan kudi ko karamar hukuma daya aka je, misali Marte ko Gujuba ko Biu ko Mongono aka zuba kudin babu abin da za su yi. Yanzu kamar ka je Bama ko Baga ko Gwoza, barnar da aka yi, wannan kudin ka zuba don su gyara gidajen mutanen da aka rusa da sauran abubuwan da suke na rayuwa na wurin, su gyara ofisoshin karamar hukuma da makarantu da sauransu, ba ka yi maganar dukiyar da ke Bama ko Baga da ta salwanta ba. Kuma dukkansu suna da manyan kasuwanni, to a je ma a ce da wannan kudin za a gina shaguna a mayar wa wadanda suka yi asara dukiyoyinsu.
Idan ka ce kana so ka je Bama ko Gwoza ko wani wurin ka gyara gidajensu kawai, ka san cewa kana da aiki. Ba wai maganar ka maido mutanen su zo su zauna sannan ka tara masu abinci na tsawon shekara daya kafin su fara sana’a ko wani abu ba, to ko karamar hukuma daya ka zuba wannan kudi babu abin da za su yi. Duk inda aka yi yaki, akwai wasu abubuwa biyu da ake yi wato a nemi inda za a zaunar da wadanda abin ya shafa, sannan kuma a yi kokari su saje cikin jama’a.
In ka lura wadannan hankalinsu ba ya jikinsu yanzu. Kag a suna bukatar kulawar likita da farko don jikinsu da hankalinsu ya dawo. Mu tuna, wasu suna kallo aka yanka miji ko mata ko uwa ko uba ko dan uwa a gabansu. Ka ga dole a samu yadda za a tsugunnar da wadannan ’yan gudun hijra.
Kuma kada ka manta ’yan gudun hijrar akwai su a Nijar da Chadi da Kamaru baya ga cikin wasu jihohimu. Ka ga ashe akwai bukatar samar da wurin zama, sannan a yi tunanin batun farfado da arzikin da suka rasa. Kuma fa duk wannan, sai an tabbatar musu cewa yakin nan fa ya kare. To ashe kuwa in haka ne, gwamnati na bukatar wani babban kasafin kudin da za ta gudanar da wannan aiki, domin ba karami ba ne. In an tuna, lokacin da aka yi Yakin Biyafara, hatta simintin da za a sake wasu gine-ginen sayo shi aka yi.
To abin da za a fara sani shi ne, shin an saka dukkan wadannan a cikin kasafin kudin da Jonathan ya yi? Domin sai Buhari ya yi akalla wajen wata shida yana amfani da wancan kasafin kudin. Ka ga ba cewa za a yi har sai badi za a fara wannan aiki ba. Don haka abin da ya kamata shi ne Buhari ya yi wani dan kasafin kudi na gaggawa domin waccan bukata da ake da ita.
Aminiya: An ce an yi waccan gidauniya ce domin fuskantar wadannan matsaloli, amma har yanzu ba a kara jin motsin komai ba har wannan gwamnati ta hau, me z aka ce?
Dokta Muri: To irin wannan gidauniya babu wani tasirin da za ta yi, kuma tunda aka yi ta babu wanda zai ce maka ga wani abu a kai, hasali ma kudin da za a ciyar da wadannan bayin Allah ake nema, wannan gidauniya siyasa ce. Ana yin ta sai kuma ita jam’iyya mai ci a lokacin, wato PDP ta ce ga tata gidauniyar. Yanzu abin da ya kamata, ga gwamnatin Buhari shi ne ta bincika ta gani saboda gidauniya ce aka yi da sunan gwamnati ba jam’iyya ko wani mutun ba. Ta bi ta gano su wane ne wannan kudi ke hannunsu domin su kawo su ta hada a cikin kasafin kudi na musamman da za ta yi.
Aminiya: Kana da ra’ayin cewa a binciki wannan kudi ke nan?
Dokta Muri: Haka! Ai kudi ne da dama daga cikin wadanda suka bayar da su suna so su ji inda suka shiga. Ko ka bayar da kudin a ce maka an yi kamfen da su? Ko wani ya sanya a aljihu ya tafi da su? Ai haka ba za ta yiwu ba. Don haka wajibi ne ga wannan gwamnati ta binciki wannan kudi da sauran kudade irin wadannan kudade da aka yi amfani da sunan gwamnati wajen nema ko tara su.
Aminiya: In har gwamnati ta yi binciken kuma a ce ta samu kudade ko akasi, me ya kamata ta yi?
Dokta Muri: In akwai su sai ta amso a hada cikin kasafin da za a yi, domin mafi yawan wadannan abubuwa sai ka ji ana wai-wai. Gaskiyar magana wannan batu ne mai sarkakiya da kowa zai so ya ji yadda aka yi. Kuma mu mun yi murna da har kuka yi tunanin bankado wannan lamari domin jama’ar kasa su ji inda aka kwana da inda za a tashi a kan batun gidauniyar tallafa wa wadanda rikicin Boko Haram ya rutsa da su da tsohuwar gwamnatin ta yi kuma har ta mika mulki ba a san matsayar kudin ba.
Aminiya: In aka ce an samu kudin shin gwamnatin Buhari za ta yi amfani da su bisa waccan manufa da tsari ko akwai wani abin da kake gani ya kamata ta yi maimakon wancan tsari?
Dokta Muri: Yana da kyau wannan gwamnatin ta kara neman gudunmawa, saboda ba ta da kudi yanzu. A kara tarawa tunda wancan akwai wadanda za su ba da wadanda suke cikin adawa amma suka ki bayarwa saboda adawa. To amma yanzu ita wannan gwamnati ta APC ita ma ta ce, a zo a tara domin aiwatar da wancan aiki. Misali, a ce kowane ma’aikaci ya bada kashi daya daga cikin albashinsa, ’yan majalisa su ba da daya bisa uku na albashinsu da sauran makamantan haka, na tabbata za a iya samun wannan gudunmawa don tallafa wa wadancan bayin Allah, musamman in aka ce Shugaban kasa ya yi wannan roko. Saboda haka yana da kyau ya sake yin wata sabuwar gidauniyar saboda waccan akwai manufarta sannan sai ya tambayi inda waccan take.
Aminiya: To in ba a samu waccan ba fa?
Dokta Muri: Sai a hukunta wadanda suka boye ta, domin ba kyalewa za a yi ba a ce, an yi ci da ceto. Ya tambayi inda suke saboda da sunan wadanda rikicin Boko Haram ya rutsa da su aka yi ta, wato mutanen Adam=awa da Borno daYobe da sauransu. Dole a bi kadin abin, a kira wadanda suka kaddamar domin jin inda aka kwana. In dan siyasa ya gudu akwai wadanda suka kaddamar da ba ’yan siyasa ba. Kuma ai akwai asusun bankin da bankin da za a kai su ajiya duk sai a nemo su, su yi bayani.
Aminiya: To ba ka ganin kamar ita jam’iyyar da ta zo ’yar adawa ce a yanzu za ta yi zargin cewa kamar wani sirri ne nata ake kokarin bankadowa?
Dokta Muri: Ai nan babu batun wani sirri, ita wannan gwamnati za ta ce za ta bude tata ce sabuwa, sannan ta ce ina kuma waccan? Saboda abin ya zama a karkashin gwamnati sai a tara a kawo su a hada. Kudi ne ba na wani sashi ba, hatta da ita gwamnatin sai an ji nawa ta ba da. Wannan ya zamo abin nan da ake cewa gwangwanin tsutsa, sai an fasa ake ganin yawansu da girmansu. Fatarmu Buhari ya zo ya yi kasafi ya kafa nasa muga irin abin da za a samu saboda a wancan lokacin akwai wadanda suka so ba da tasu gudunmawar amma abin bai yiwu ba saboda suna adawa, to, yanzu dama ta samu, sai a hada a ga me za a yi.
Aminiya: Mu dauka cewa wadannan abubuwa sun samu, wace hanya kake gani za a bi don tallafa musu?
Dokta Muri: Ai wannan ya wuce tallafi, ’yan kasa ne kuma suna da hakki a cikin dukiyar kasa. Saboda haka gwamnati za ta yi kasafin kudi bisa hasashen irin gudunmawar da za a tara da wadda aka tara ta mika wa majalisa domin amincewa don ci gaba da aiwatar da abubuwan da suka kamata a wadancan yankuna. Misali, yin muhalli, sai yakuwar neman dangi domin su hadu don mayar da su gidajensu.
Bayan tun farko an dauki matakan tsaro, sai kuma batun abinci da kiwon lafiyarsu tare kuma da batun ilimi. Koda kuwa za a yi wurare ne na wucin-gadi kafin a gyara gidajensu. Kuma wannan duk hakki ne na gwamnati domin ’yan kasa ne kuma gwamnatin ce tun farko ta yi sakaci har hakan ya faru.
Aminiya: Ke nan akwai kabubale ga wannan sabuwar gwamnati?
Dokta Muri: Ai kalubalen ba su da iyaka, amma wannan shi ne muhimmi domin wanda ya tagayyara shi ake fara kulawa da shi. To bayan an aiwatar da wadancan abubuwa sai batun sana’a da sauransu.
Aminiya: To su kansu ’yan kasa akwai wata rawar da kake gani za su taka?
Dokta Muri: kwarai. Mu dauki kowace karamar hukuma a ce misali tana samun karanci Naira miliyan 60 zuwa 80 a kowane wata, sai a ce ta raba wannan kudi kashi biyu, rabi don tsugunar da wadannan mutane, rabi kuma don ayyukan yau da kullum a wurare da abin ya shafa. Kuma wani abin tambaya shi ne, ina kudaden kananan hukumomin da aka tarwatsa a wadannan yankuna da ake fitarwa daga asusun tarayya a kowane wata? Yaya ake yi da su tunda an wargaza kananan hukumomin? Ka san dai ba za a ce Gwamna ya kashe kudaden ba tun da shi ma nasa suna cikin wani hali. In ka lura fa, girman kasar da ta tarwatse a wannan yankin da abin ya shafa ya kai girman kasar Isra’ila. Saboda haka sai an gano kudinsu inda suka shiga kuma fa na sama da shekara daya ko biyu domin wasu tuni suka yi gudun hijra. Wadannan kudi ne ya kamata a fara aiki da su kafin kasafin da gwamnati za ta yi a yanzu.
Aminiya: Yanzu wace shawara ke gare ka?
Dokta Muri: Shawarar da nake da ita ita ce a yi kokari gwamnati ta bada cikakkiyar kariya da tsaro a wadannan wurare sannan a yi maganar mutanen da ya kamata a ce kowa yana cikin gidansa. Sannan a samu hukumar kidaya ta kasa domin tantance yawan mutanen da suka rage da wadanda aka rasa daga kowace karamar hukuma da wannan bala’i ya shafa. Ta haka ne za a kara gane irin halin da wannan matsala ta Boko Haram ta haifar.