Ya kamata Buhari ya waiwayi masu jefa jama’a a cikin kunci –Dokta Baninge

Sarkin Maganin Masarautar Ningi a Jihar Bauchi da ke zaune a garin Jos a Jihar Filato, Dokta Ibrahim Baninge ya bukaci gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta tashi tsaye wajen maganin masu yi mata zagon-kasa da suke jefa jama’a a cikin mawuyacin hali da kunci a kasar nan. Dokta Ibrahim Baninge ya bayyana haka ne […]

Ya kamata Buhari ya waiwayi masu jefa jama’a a cikin kunci –Dokta Baninge
Ya kamata Buhari ya waiwayi masu jefa jama’a a cikin kunci –Dokta Baninge

Sarkin Maganin Masarautar Ningi a Jihar Bauchi da ke zaune a garin Jos a Jihar Filato, Dokta Ibrahim Baninge ya bukaci gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta tashi tsaye wajen maganin masu yi mata zagon-kasa da suke jefa jama’a a cikin mawuyacin hali da kunci a kasar nan.
Dokta Ibrahim Baninge ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Jos, inda ya ce “A gaskiya ana yi wa gwamnatin Buhari zagon-kasa, a fannin harkar man fetur da wutar lantarki da harkokin kasuwanci a kasar nan, domin a dada jefa al’ummar kasar nan a cikin
mawuyacin hali. Wasu miyagun’yan Najeriya ne da suke bakin ciki da hawa mulkin Shugaban kasa Muhammadu Buhari suke yi wa gwamnatin zagon-kasa.”
Dokta Baninge ya ce ya kamata Shugaban kasa ya waiwayi wadannan al’amura, domin gano
wadanda suke kawo matsalolin domin ya dauki mataki a kansu.
Dokta Baninge ya yi kira ga ’yan Najeriya su ci gaba da yin addu’o’in Allah Ya taimaki wannan gwamnati domin ta samu damar ceto talakawan kasar nan daga mawuyacin halin da suke ciki.