Ya kamata dattawan Kirista su rika jan hankalin shugabannin CAN – Dokta Jalo

Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa Dokta Ibrahim Jalo Jalingo ya bukaci dattawan Kiristocin kasar nan su rika jan hankalin shugabannin kungiyar Kiristoci ta kasa (CAN) dangane da kalaman nuna kiyayya ga Musulmin da suke yi, musamman ga wadanda ke cikin wannan gwamnati. Dokta Ibrahim Jalo Jalingo ya […]

Ya kamata dattawan Kirista su rika jan hankalin shugabannin CAN – Dokta Jalo
Ya kamata dattawan Kirista su rika jan hankalin shugabannin CAN – Dokta Jalo

Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa Dokta Ibrahim Jalo Jalingo ya bukaci dattawan Kiristocin kasar nan su rika jan hankalin shugabannin kungiyar Kiristoci ta kasa (CAN) dangane da kalaman nuna kiyayya ga Musulmin da suke yi, musamman ga wadanda ke cikin wannan gwamnati.

Dokta Ibrahim Jalo Jalingo ya bayyana haka ne a wata sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi don mayar da martani ga kiran da Babban Sakataren kungiyar CAN, Rabaran Musa Asake ya yi cewa Ministan Tsaro Janar Aliyu Gusau (mai ritaya) da Mashawarcin Shugaban kasa kan Harkokin Tsaro, Kanar Sambo Dasuki su yi murabus, saboda sun kasa magance ta’addancin da ake yi a kasar nan.
Dokta Jalo Jalingo ya nuna takaici kan yadda Sakataren ya alkanta mayakan Boko Haram da Musulmin da ba su da wata manufa face hallakar da duk Kiristocin yankin da tsaida wata daular Musulunci da ba jama’a ne suka zabe ta ba.
Dokta Jalo ya ce, sananne ne cewa mayakan Boko Haram ba suna wakiltar Musulmin Najeriya ba ne, kuma ba su kyale Musulmi ba wajen aiwatar da miyagun ayyukansu.
Dokta Jalingo ya ce kalaman Rabaran Asake na nuna rashin kaunarsa ga ci gaba da dunkulewar Najeriya a matsayin kasa guda, “Kuma da ban takaici shugabannin CAN su ce sun kasa fahimtar bambancin da ke tsakanin “Addinin Musulunci” da barnar da ’yan Boko Haram ke yi.
Ya ce ’yan Boko Haram sun kashe manyan malaman Musulunci da yawa, kuma ’yan matan Chibok da suka sace ba su ware Kirista suka bar Musulmi ba.
“Duk mai hankali da bibiyar lamura ya san cewa shugabannin Najeriya ba sa yin abin da ya kamata domin tabbatar da tsaro. Kuma yana sane da barnar da ta bazu cikin jami’an gwamnati: sojoji da farar hularsu. Saboda haka da Sakataren CAN da sauran shugabannin da yake magana da muryarsu mutane ne masu kaunar Najeriya, ba masu nuna kiyayya ga Musulmi ba, to, abin da ya kamata ya yi, shi ne ya yi kira ga gwamnatin ta yi murabus: Musulminta da wadanda ba Musulmi ba, Shugaban kasa da duk masu taimaka masa. Daga nan sai a kafa gwamnatin riko da za ta dawo da zaman lafiya a cikin kasa,” inji Dokta Jalingo.

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya

Gwamnatin Tinubu na yunƙurin hana ni yin takara — Peter Obi

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi