Ya kamata duk dan kasa ya shiga siyasa-Bishop Onaiyekan
Shugaban Katolika bangaren Abuja, John-Cardinal Onaiyekan ya bukaci duk ’yan Najeriya su shiga siyasa don su bunkasa ci gaban kasa cikin sauri. Onaiyekan ya yi kiran yayin da yake murnar bikin cika shekaru 35 na matsayinsa na Bishop wanda aka gudanar a cocin Our Ladi da ke Abuja, a ranar Asabar din da ta […]

Shugaban Katolika bangaren Abuja, John-Cardinal Onaiyekan ya bukaci duk ’yan Najeriya su shiga siyasa don su bunkasa ci gaban kasa cikin sauri.
Onaiyekan ya yi kiran yayin da yake murnar bikin cika shekaru 35 na matsayinsa na Bishop wanda aka gudanar a cocin Our Ladi da ke Abuja, a ranar Asabar din da ta gabata, a Abuja.
Ya shawarci ’yan siyasa su rika tallafa wa jama’a bisa gaskiya da rikon amana da kuma tsoron Allah sannan ya yi kira ga ’yan Najeriya su shiga siyasa.