Ya kamata gwamnati da kamfanoni su zuba jari a Kannywood- Darakta Kamal
Fitaccen daraktan fina-finan Hausa, Kamal S. Alkali ya bukaci gwamnati da kamfanoni su zuba jari a masana’antar fina-finan Hausa (Kannywood) don masana’antar ta rika tafiya da zamani don kuma ta yi gogayya da sauran takwarorinta na duniya.Ya ce idan aka duba tuni sauran masana’antun fina-finan duniya suka bunkasa ta hanyar amfani da kayan aiki masu […]

Fitaccen daraktan fina-finan Hausa, Kamal S. Alkali ya bukaci gwamnati da kamfanoni su zuba jari a masana’antar fina-finan Hausa (Kannywood) don masana’antar ta rika tafiya da zamani don kuma ta yi gogayya da sauran takwarorinta na duniya.
Ya ce idan aka duba tuni sauran masana’antun fina-finan duniya suka bunkasa ta hanyar amfani da kayan aiki masu inganci da kuma kawo labarai masu kayatarwa da ilimantarwa da kuma nishadantarwa.
“Babu abin da ya ba ni mamaki kamar lokacin da nake bincike a kan fim din ‘Game of Thrones’, sai na ga an je kasashe arba’in da suka hada da Scotland da Belgiyum da Ingila da Kanada da Rasha da sauransu don a samu lokashen daya kawai, wato wurin da za a samar da masarauta a cikin fim din, hakan ya kayatar da ni. Don haka ya kamata mu ma ‘yan fim din Hausa mu tashi tsaye don mu tafi da zamani, duk da cewar kyamarar da muke amfani da ita yanzu a Kannywood da ita ake amfani a masana’antar fim ta Hollywood, amma akwai bukatar mu kara zage damtse don kada a bar mu a baya.” Inji shi.
Ya bukaci gwamnati da sauran kamfanoni su rika tallafa wa ‘yan fim don a samu ci gaban da ake bukata.
“Idan ka duba fina-finan Indiya kawai za ka ga kamfanoni masu yawa ne ke tallafawa, inda ake samun riba mai yawa, kuma ake samar da fina-finai masu inganci, ba wai na ce mu kwaikwayi Indiya ba ne, a’a, amma a ko’ina ka ga an yi abu mai kyau za ka iya koyi da shi. Don haka ya kamata kamfanoni da gwamnati su taimaka ta hanyar zuba jari ko tallafawa ta kowane bangare don masana’antar Kannywood ta ci gaba.” Inji Kamal.