‘Ya kamata gwamnati ta dauki fyade barazanar tsaro’

Hadakar Kungiyoyin Kare Hakkin Bil’Adama (CSOs) a fannin tsaro da shari’a, ta yi kira ga Gwamnatocin Jiha da na Tarayya da kuma ‘yan sanda da su dauki karuwar fyade da sauran cin zarafin mata da ake samu a Najeriya matsayin barazanar tsaro. Kungiyoyin a karkashin inuwar Justice and Security Dialogue (JSD) sun kuma bukaci ‘Yan […]

‘Ya kamata gwamnati ta dauki fyade barazanar tsaro’

Fyade

Hadakar Kungiyoyin Kare Hakkin Bil’Adama (CSOs) a fannin tsaro da shari’a, ta yi kira ga Gwamnatocin Jiha da na Tarayya da kuma ‘yan sanda da su dauki karuwar fyade da sauran cin zarafin mata da ake samu a Najeriya matsayin barazanar tsaro.

Kungiyoyin a karkashin inuwar Justice and Security Dialogue (JSD) sun kuma bukaci ‘Yan Najeriya da su kalli matsalar fyade ta fuskar nakasu ga cigaban kasa.

Shugaban kungiyar Isioma Kemakolam, ta ce aikata fyade na ci gaba a kasar ne saboda har yanzu gwamnati ba ta dauke shi barazanar tsaro ba.

Isioma ta ce matsalar COVID-19 ta bayyanar da matsalar fyade karara tare da wayar da kan jama’a, amma idan har ana son a samu sauyi to dole sai gwamnati da ‘yan sanda sun dauki fyade matsalar tsaro domin kawo wa al”umma mafita.

Ta kuma ce kungiyar ta gudanar da abubuwa daban-daban a kasar nan wadda daga ciki har da teburin kula da hakkokin mata da ta ajiye Ofishin ‘Yan sanda da ke Nasarawa.

Ta kuma yi kira ga mutane da su yi amfani da Teburi domin kai kokensu da bayyana yanayin da suka samu kansu.

Matsalar Tsaro: Dole mu faɗakar da mutane yadda za su kare kansu – ACF

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna