Ya Kamata Gwamnati Ta Dinga Tunawa Da Mata A Shirye-shiryenta Na Noma —ASSAPIN
Shugabar Kungiyar kananan manoman Najeriya reshen Jihar Bauchi (ASSAPIN), Hajiya Amina Jibrin ta ce ya dace gwamnati ta dinga sanya mata a jerin masu cin gajiyar shirye-shiryenta na noma domin samun sakamako mai kyau. Hajiya Amina ta yi kiran ne a taron bikin ranar Abinci ta Duniya da aka gudanar a Bauchi. Matawalle ya nemi […]
Shugabar Kungiyar kananan manoman Najeriya reshen Jihar Bauchi (ASSAPIN), Hajiya Amina Jibrin ta ce ya dace gwamnati ta dinga sanya mata a jerin masu cin gajiyar shirye-shiryenta na noma domin samun sakamako mai kyau.
Hajiya Amina ta yi kiran ne a taron bikin ranar Abinci ta Duniya da aka gudanar a Bauchi.
- Matawalle ya nemi afuwar kafofin yada labaran da ya rufe
- Saurayi ya bace shekara 3 bayan bacewar dan uwansa a Kano
Baya ga haka kuma ta yi kira da a tallafa wa manoman, musamman a wannan lokacin, la’akari da yadda ambaliyar ruwa a bana ta sanya su asara.
Ta ce kiran ya zamo dole domin manoman na bukatar taimakon gwamnati da al’umma, wajen farfado da nomansu, domin ta haka ne za su ci gaba da samar da wadataccen abinci ga al’umma.
“Akwai bukatar samar da dokoki da tsare-tsaren da za su bai wa kananan manoma damar samun inshora da kuma wayar da kansu kan muhimmancin hakan.
“Gwamnatin jiharmu ya kamata ta kirkiri hukumar da za ta zaburar da mutane su yi noma, karkashin shirinta na cigaban kananan manoma”, in ji ta.
Hajiya Amina ta kuma yi kira ga gwamnatin da ta ware kaso sittin na kasafin kudinta kamar yadda yake a yarjejeniyar Maputo da Gamayyar Kungiyar Kasashen Afrika AU ta yi a shekarar 2003.