‘Ya kamata gwamnati ta kama Asari Dokubo’

Wani shugaban matasa da ke Jos a Jihar Filato Malam Abu Zarri Sani Muhammad ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta kama tsohon shugaban matasa kabilar Ijaw, Mista Asari Dokubo kan irin miyagun kalaman da yake yi, wadanda za su iya kawo rikici a kasar nan. Malam Abu Zarri Muhammad ya yi wannan kiran ne a lokacin […]

‘Ya kamata gwamnati ta kama Asari Dokubo’
‘Ya kamata gwamnati ta kama Asari Dokubo’

Wani shugaban matasa da ke Jos a Jihar Filato Malam Abu Zarri Sani Muhammad ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta kama tsohon shugaban matasa kabilar Ijaw, Mista Asari Dokubo kan irin miyagun kalaman da yake yi, wadanda za su iya kawo rikici a kasar nan.
Malam Abu Zarri Muhammad ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Jos, inda ya ce idan har ba da hannun gwamnati Asari Dokubo yake irin wadannan miyagun maganganu na tayar da hankali a kasar nan ba, to ya kamata gwamnatin ta kama shi.
Abu Zarri ya ce Dakubo ya taba cewa matukar Shugaba Jonathan bai sake cin zabe a 2015 ba, za a zubar da jini a kasar nan, kuma ga shi a ’yan kwanakin nan, ya sake fitowa yana magangannun banza kan harin da aka kai wa tsohon Shugaban kasa Janar Muhammad Buhari.
Ya ce gaskiya irin wadannan maganganu da Dokubo ke yi na nuna cewa shi dan ta’adda ne, don haka ya kamata gwamnati ta kama shi.
“Mu ’yan Arewa ba tsoronsa muke yi ba, domin duk abin da yake gadara da shi muna gadara da shi. Kuma abubuwan da ake yi mana a Arewa muna hakuri ne, amma mun ga abin na neman wuce iyaka, don haka Dokubo ya guji takalar Arewa, domin duk ranar da ’yan Arewa suka tashi maida martani zai raina kansa,” inji shi.
Ya ce ya kamata mutanen kasar nan su san cewa idan masifa ta tashi za ta iya shafar kowa a kasar nan, don haka ya kamata su hada kai su zauna lafiya.

An fara sana’ar hayar Fawa-bank a Kano

’Yan sanda sun kama fasinja ya ɓoye bindiga a cikin burodi 

An kama fasto kan kashe ’yar shekara 13 da duka

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya