Ya kamata gwamnati ta kara kaimi kan matsalar tsaro – Rarara
Mawakin ya ce a yanzu addu’ar samun zaman lafiya Najeriya ta fi bukata
Fitaccen mawakin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, kuma shugaban kungiyar 13×13, Dauda Kahutu Rarara ya jajanta wa mutanen Najeriya bisa ibtila’in da suke fuskanta na rashin tsaro a fadin kasar.
Rarara ya bayyana hakan ne a sakon
kungiyar na Ramadan da ya fitar a wani faifan bidiyo da Aminiya ta gani, inda a ciki ya ce, “Muna jajanta wa al’ummar Najeriya musamman ‘yan Arewa.
- Sojojin Isra’ila sun kashe Bafalasdine, sun jikkata wasu mutum 13
- Ramadan: A wanne hali Musulman Ukraine suke azumi a yanayin yaki?
“Muna rokon Aallah Ya kawo mana zaman lafiya, amin. Muna amfani da wannan damar wajen taya al’ummar
Musulumi baki daya barkanmu da shigowa watan Ramadan mai albarka.
A cikin bidiyon, mawakin ya bayyana
cewa, “Muna alhini da jajanta wa mutanen Najeriya game da ibtila’in da ke faruwa a sassa na kasarmu.
“A matsayina na shugaban kungiyar 13×13, ina kara kira ga gwamnati a matakin kasa da jihohi da su kara kaimi wajen inganta tsaro domin samun zaman lafiya mai dorewa.
“Muna amfani da damar wannan wata
mai albarka wajen yin addu’ar Allah Ya ba mu zaman lafiya. Allah wadanda suke shirya wannan abu da gangan ka san su, idan akwai masu shiryuwa ka sani, idan ba masu shiryuwa ba ne, ka san yadda za ka yi da su.”