Ya kamata gwamnati ta taimaka wa manoman asali – Shugaban Kungiyar Alarammomi Manoma

Alaramma Nuhu Baba Tanko Jama’a, shi ne Shugaban kungiyar Alarammomi Manoma ta Jihar Kaduna. A tattaunawarsa da Aminiya, ya bayyana dalilinsu na kafa kungiyar da kuma yadda take tafiyar da harkokinta, inda ya karkare da kira ga gwamnati, domin ta tallafa wa manoma na gaskiya. Ga yadda tattaunawar ta kasance: Da farko muna so ka […]

Ya kamata gwamnati ta taimaka wa manoman asali – Shugaban Kungiyar Alarammomi Manoma
Ya kamata gwamnati ta taimaka wa manoman asali – Shugaban Kungiyar Alarammomi Manoma

Alaramma Nuhu Baba Tanko Jama’a, shi ne Shugaban kungiyar Alarammomi Manoma ta Jihar Kaduna. A tattaunawarsa da Aminiya, ya bayyana dalilinsu na kafa kungiyar da kuma yadda take tafiyar da harkokinta, inda ya karkare da kira ga gwamnati, domin ta tallafa wa manoma na gaskiya. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Da farko muna so ka gabatar mana da kanka.
To, ni sunana shi ne Nuhu Tanko amma an fi sani na da Malam Baba Tanko Jama’a.
Mene ne matsayinka a wannan kungiyar?
Ni ne shugaban wannan kungiya da ake kira Alarammas
Farmers’ Debelopment Association ta Jihar Kaduna gaba daya. Wannan ya biyo bayan wani horo ne da aka ba mu karkashin wata kungiya mai suna ‘Shirin Tallafa Wa Sashen Ilmi A Najeriya’ wato ‘Education Support Programme In Nigeria (ESSPIN)’ wacce take reshe ce karkashin gidauniyar UKAID ta kasar Birtaniya.
Bayan sun ba mu horo kan yadda za mu yi noma na tsawon kamar shekara hudu sai suka ga za mu iya tsayuwa da kafafunmu, sai suka yaye mu. Daga nan aka zabe ni a matsayin shugaban wannan kungiya na jiha.
Tun wace shekara aka kafa wannan kungiya?
Gaskiya ta dade da kafuwa amma dai mun yi mata rijista ne a watan Janairun shekarar 2013.
Mene ne muhimman ayyukan wannan kungiya?
Da yake dai har yanzu ba mu gama kama kasa ba tukuna amma daga cikin muhimman ayyukanmu shi ne rungumar harkar noma gadan-gadan, musamman ganin cewa dama alarammomi manoma ne da makiyaya. To hakan shi ne zai taimaka mana wajen dogaro da kanmu da kuma dakile yawan barace-barace.
Amma ba ka ganin shigarku cikin harkar noma gadan-gadan ba zai takaita harkar karantarwa ba?
A’a, shi fadawa cikin harkar noma ba zai takaita karantar da karatu ba, domin shi dama malami in dai mazaunin wuri ne tuntuni ba ka rasa shi da gona, wacce a cikinta ne yake dan samun abin tabawa da shi da wanda ke karkashinsa.  Don haka ba abin da zai hana su harkar karantar da karatunsu, domin shi noman nan bai fi kwana uku a sati ba kuma ba dukkanin wuni ake cinyewa a gona ba.
To, bayan ita wannan kungiya (ESSPIN) ta gama ba ku horo, akwai wani tallafi ne da ta ba ku kamar na kudi da kayan noma ne don ganin kun fada harkar sosai, kasantuwar noma na bukatar kashe kudi?
E, ta taba ba mu taki kyauta da nake jin kowanne alaramma ya samu buhu hudu na taki da maganin feshi da kuma iri na shuka. Da muka yi noman shekara guda sai suka ce mu adana. To bayan sun zo sun gani kamar yadda muka yi da su, sai suka ware wasu suka ce mu sayar da su. To, bayan an sayar, alal akalla kowane alaramma ya ware buhu goma cikin abin da ya samu, sai aka ba shugaban (ni ke nan) kudin na kai wa ESSPIN. Kamar mu a Karamar Hukumar Jama’a mun kai kudi kimanin Naira dubu 120. Da muka kai masu, shi ne suka bude mana asusun ajiya a banki.
Wannan kungiya tana da kamar mambobi guda nawa?
Akwai alarammomi da yawa, sai dai har yanzu muna kiran sauran wadanda ba su sani ba, su zo su shiga wannan kungiyar. Ni daga Karamar Hukumar Jama’a, ni ne shugaba, sakatarena kuma yana Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa ne, Kawo, wato Malam Ja’afar dan Malam Musa Kawo, Shugaban kungiyar Makarantun Allo ta Jihar Kaduna, mataimakina kuma dan karamar Hukumar Kaciya ne, wato Malam Ahmadu Ibrahim. Ba mu da adadin alkaluma amma dai muna da wakilci a kananan hukumomin Kaduna ta Kudu da ta Arewa da Karamar Hukumar Kagarko da Igabi da Jaba da kuma Zangon Kataf da sauran wurare.
Akwai takamaiman wani abu ne da kuka fi mayar da hankali wajen nomawa ne?
A’a, sai dai kowane sashi na Jihar Kaduna akwai abin da suka fi nomawa. Ka ga kamar Arewacin Kaduna, hatsi suka fi nomawa, yayin da mu kuma a Kudancin Kaduna muka fi noma citta amma masarar da muke nomawa ba ta wuce iya wadda za mu ci ba kawai.
A karshe ko akwai wani korafi ko wani kira da kuke da shi ga gwamnati?
E, kiranmu dai kawai shi ne, duk irin tallafin da muke jin gwamnati tana bayarwa, gaskiya ba ya zuwa hannunmu manoma, sai dai ya fada hannun wasunmu, sai dai mu ji a kafafen watsa labarai, amma yanzu muna rokon don Allah gwamnati ta waiwaye mu, ta taimaka mana domin shi ne zai sa mu dogara da kanmu har ma mu rike wadanda ke karkashinmu.

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50 a Kaduna

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54