Ya kamata gwamnati ta zamanantar karatun tsangaya —Mujahid Baure

Malamin ya ce ya kamata gwamnati ta ba almajiyar kulawa kamar kowane dan Njeriya.

Ya kamata gwamnati ta zamanantar karatun tsangaya —Mujahid Baure

Wani malamin addinin Islama a Gombe, Alaramma Mujahid Ibrahim Baure, bukaci Gwamnatin Tarayya da ta zamanantar da makarantun tsangaya tare da gina sabbi a yankin Arewa.

Da yake jawabi a wajen Tafsirinsa da yake gabatarwa a massallacin garin Kwadom da ke Karamar Hukumar Yamaltu Deba, a Jihar Gombe,  malamin ya bayyana cewa Almajirai ba ’yan ta’adda ba ne, don haka a daina kyamar su.

A cewarsa almajirai ma ’yan kasa ne kamar yadda kowane dan Najeriya ya cancanci a taimaka wa kuma a rika shigar da su duk wani tsarin gwamnati domin suma su amfana.

Mujahid Baure, ya kuma yaba wa Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na jihar kan yadda ya aza tubalin gina katafariyar tsangayar Goni Sani da ke garin Gombe zuwa ta zamani.

A cewar malami, duk wani mai kaunar ci gaban almajirai su ma suna kaunar shi kuma za su yi ta mishi addu’ar alkhairi.

Ya kuma ce a almajirai a Gombe sun yi sa’a, Sanata Muhammad Danjuma Goje, yana sanya fitulu masu aiki da hasken rana a tsangayoyi, matarsa kuma tana raba musu abinci.