Ya kamata Gwamnatin El-Rufa’i ta waiwaye mu – Sarkin Samarin Jama’a

Sarkin Samarin Masarautar Jama’a da ke Jihar Kaduna Alhaji Mudi Shafi’u Tahir, ya yi kira ga gwamnatin jihar a karkashin Gwamna Nasir El-Rufa’i ta cika alkawarin da ta dauka cewa za ta yi adalci wajen yin ayyuka da rabon mukamai ba tare da nuna bambamcin kabila ko addini ba musamman a Kudancin Kaduna.Sarkin Samarin, ya […]

Ya kamata Gwamnatin El-Rufa’i ta waiwaye mu – Sarkin Samarin Jama’a

Sarkin Samarin Masarautar Jama’a da ke Jihar Kaduna Alhaji Mudi Shafi’u Tahir, ya yi kira ga gwamnatin jihar a karkashin Gwamna Nasir El-Rufa’i ta cika alkawarin da ta dauka cewa za ta yi adalci wajen yin ayyuka da rabon mukamai ba tare da nuna bambamcin kabila ko addini ba musamman a Kudancin Kaduna.
Sarkin Samarin, ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da Aminiya a garin Kafanchan, inda ya ce “Lokacin da Gwamna Nasir El-Rufa’i ya zo yakin neman zabe a Kudancin Kaduna mu Hausawa da Fulani mu muka karbe shi muka yawata da shi muka tallata shi kuma kuri’unmu, musamman na cikin garin Kafanchan sun yi tasiri matuka a yankin Kudancin Kaduna wajen zabensa, amma abin takaici koda ya tashi rabon mukamai sai ya kwashe gaba daya ya bai wa ’ya’yan wata kabila alhali ya ce ba zai ware wasu daban ba. Kuma ga shi ba wani aiki da muka soma gani kuma ba mu da wani kwamishina da a ka zaba daga cikinmu sai aka ba ’yan kabilar Kagoma kwamishinoni biyu sannan aka sake dauko dansu aka ba shi Shugaban karamar Hukumar Jama’a da Sakataren Ilimi.           
Sarkin Samarin ya yi kira ga Gwamna El-Rufa’i ya yi musu ayyukan da suka dace a cikin garin Kafanchan da suka hada da gyaran hanyoyin cikin gari da sanya wutar kan hanya da gina babbar kasuwar Kafanchan da gyara hanyar makabarta da fitar da magudanun ruwa da kuma samar da ayyukan yi ga matasa, domin rage zaman kashe wando.
Ya ce, akwai bukatar ya yi wadannan ayyuka a garin wanda shi ne cibiyar Kudancin Kaduna koda kuwa wasu kabilun yankin za su ce yana fifita kabilarsa, “Suna amfani da irin wadannan kalmomi ne kawai don siyasa da firgita shugaba su jawo hankalinsa zuwa gare su, mu muke tare da su mun san su haka salon siyasarsu take alhali sun manta da isgilancin da suke mana lokacin da muke cewa ‘Sai Buhari,’ ‘Sai El-Rufa’i,’ amma sai ga shi yanzu sun fi mu amfana da gwamnatin. Mu ba muna cewa gwamnati ta fifita mu a kan wasu ba ne, amma a rika yin adalci kuma a matsayinmu na wadanda suka yi ruwa da tsaki a kan zabensa bai kamata mu tashi a tutar babu ba, ba mu ga tsuntsu ba mu ga tarko,” inji shi.